✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Jam’iyyar APC na Oya ya mutu a Amurka

Shugaban ya shafe kusan shekara guda yana jinya a Amurka.

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Oyo, Isaac Omodewu, ya rasu.

Rahotanni sun bayyana cewar ya rasu ne a ƙasar Amurka.

Omodewu, ya bar Najeriya a watan Nuwamban 2023, domin neman lafiya.

Sai dai ya rasu bayan shafe kusan shekara guda yana jinyar cutar da ba a bayyana sunanta ba a Amurka.

Sakataren Yaɗa Labaran APC a Jihar Oyo, Olawale Sadare ne, ya tabbatar da rasuwar a ranar Litinin.

“Shugabanmu ya mutu,” in ji shi.

Omodewu, wanda ya fito daga Otu a ƙaramar hukumar Itesiwaju ta Jihar Oyo, ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishina a gwamnatin marigayi tsohon Gwamnan jihar, Abiola Ajimobi.

A baya-bayan nan, ya kammala karatunsa na makarantar lauyoyi.