Shugaban Jami’ar NOUN, Farfesa Abdalla Uba Adamu ya kaddamar da sabuwar hanyar yin gudanar da jarrabawa ta gaba ta amfani da Intanet da ya bullo da ita.
Sabuwar hanyar ana fata a gabatar da ita lokacin fara jarrabawa ta makon gobe domin yin jarrabawa ta Intanet a fadin kasar nan, kuma an tsara ce domin a dada saukaka yadda ake gudanar da jarrabawar da magance matsalolin bacewar sakamakon jarrabawa da kuma rage kudin da ake kashewa wajen gudanar da jarrabawar.
A wajen taron bitar da aka shirya don gabatar da sabuwar hanyar Farfesa Adamu ya ce, sabuwar hanyar wani aikin hadin gwiwa ne na ofisoshin tattara bayanai (MIS) da na Kimiyyar Sadarwa (ICT) da kuma na Tsara Jarrabawa (DEA) na jami’ar.
Taron ya mayar da hankali kan bayar da horo da nuna wa ma’aikatan sassa yadda ake amfani da sabuwar hanyar da yadda za a yi aiki da ita a jarrabawa mai zuwa.
Shugaban Jami’ar ya yaba wa sassan kan kokarin da suka yi wajen tabbatar da fito da sabuwar hanyar tare da gudanar da ita. Kuma ya jinjina musu kan yin aiki tare inda ya nuna irin muhimmancin da suke da ita a jami’ar a matsayinsu na cibiyar sadarwa ta Intanet.
Shugaban Jami’ar ya ce, sabuwar hanyar “Wani karin ci gaba ne ga jami’ar a yunkurinta na dogara da kanta daga yadda al’amura suke gudana a baya. Mun shirya don ci gaba da gwaji da kuma aiki da sabuwar hanyar har sai an cimma nasara.”
Sabuwar hanyar a cewar Shugaban Jami’ar ba a taba amfani da ita ba a jami’ar don haka ya nanata muhimmancin auna karfi da rashin karfin aikinta a wurin bitar.
Lokacin da yake jawabin bude taron Daraktan Kimiyyar Sadarwa (DICT), Dokta Madu Galadima ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Jami’ar kan gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen kaddamar da sabuwar hanyar, kuma ya ba shi tabbacin cewa sashinsa zai yi duk abin da zai iya wajen tabbatar da jarrabawar ta Intanet ta gudana sumui-lumui.
Daraktan MIS, Dokta Mukhtar Alhassan ya yaba wa ayarin ma’aikatan kan sadaukar da kan da suka nuna wajen kirkiro wannan sabuwar hanya inda ya bayar da tabbacin cewa sashinsa yana aiki kafada-da-kafada da DICT da DEA domin tabbatar da sun samar da mafita ga duk wata matsala da za ta iya tasowa a gaba.