✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban IPMAN ya koka da rashin gaskiyar abokan hulda

Kungiyar Dillalan Man fetur masu zaman kan su  ta kasa IPMAN reshen Jihar Kuros Riba ta koka kan irin yadda wasu kamfanonin da ke sayar…

Kungiyar Dillalan Man fetur masu zaman kan su  ta kasa IPMAN reshen Jihar Kuros Riba ta koka kan irin yadda wasu kamfanonin da ke sayar musu da albarkatun man fetur  ke nuna halin rashin dattaku, a cewar Alhaji Isah Umar,   daya daga cikin ’yan kasuwar da ya  sayi kaya kan  farashi,  amma daga bisani saboda kayan farashinsa ya karu kamfanin da ya  saya ya nemi tilasta masa sai ya dora kudin da suka karu bayan ya sayi kayan kafin ya dauka.

Alhaji Umar wanda yayi tir  da halayen kamfanin sayar da mai na  Samson dangane da karin kudin da yayi masa, ya sanya tilas ya biya, don haka a zantawar sa da  Aminiya ya ce: “Abin mamaki na sayi man fetur kan farashi, amma da yake kafin in dauki kayan an samu karin Naira biyu akai sai kamfanin ya ce ba zai ba ni mai ba, har sai na dora wannan karin Naira biyu da aka samu akai kafin a ba ni kaya”. Lamarin dai dan kasuwar  ya tubure kan cewa ba zai kara ko kwandala akai ba.

Ya ci gaba da cewa daga nan har matatar mai ta Warri idan aka sayi kaya indai kafin mutum ya dauka aka samu karin farashi ko da na sisin kwabo ne sai su ce sai mai kaya ya biya kafin a ba shi wanda hakan “ba adalci ba ne, “ inji shi. Wannan ja-ni-in-ja-ka da ke faruwa tsakanin Alhaji Isah Umar da kamfanin Samson masu daffon  ajiye man fetur suna sayarwa da lasisin gwamnati ya tabbatar da cewa matukar  ’yan kasuwa masu hali irin na wancan kamfani ba su sauya tunanin su ba suka rika kamanta gaskiya, to nan gaba fa ba za su kai labari ba.

D a wakilin mu ya tuntubi Mista Ugochukwu mataimakin manajan sayar da mai na  kamfanin domin jin ta bakinsa game da lamarin ya zuke ya ce: “Ni  ba ni da ikon yin magana da ’yan jarida, amma kayan su da suka saya za a ba su.” Sai ya kashe wayarsa.

Kamfanin mai na  Northwest masu hada-hadar man fetur ne kadai suka ciri tuta a wajen kamanta gaskiya a harkokin su na kasuwa, kamar yadda Alhaji Isah Umar ya tabbatar wa manema labarai da suka garzaya kamfanin domin jin yadda lamarin ya  gudana tsakanin su.