✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban EFCC ya yanke jiki ya fadi a Fadar Shugaban Kasa

Pantami da wasu manyan baki ne suka dauke Abdulrasheed Bawa a wurin.

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya yanke jiki ya fadi a yayin da yake jawabi a wani taro a Fadar Shugaban Kasa.

Bawa na cikin jawabi a taron na ranar Alhamis ne aka ji ya dan yi shiru, jim kadan kuma sai ya sa hannu ya kare fuskarsa, ya ce a yi masa hakuri ba zai iya ci gaba da jawabi ba.

A nan ne Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, da wasu manyan jami’an gwamnati da ke halartar taron suka tashi suka rike shi za su zaunar da shi.

Ana cikin haka ne Bawa ya yanke jiki ya fadi a zauran taron da aka shirya kan karbar katin shaidar dan kasa.

Daga nan aka fice da shi daga Fadar Shugaban Kasar kafin daga bisani Pantami ya dawo dakin taron inda ya bayyaan cewa shugaban na EFCC yana cikin koshin lafiya.