Dalibin da ’yan bindiga suka kashe a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya Shugaban dalibai ne a makarantar.
Ahmad Muhammad, shi ne Shugaban Kungiyar Dalibai Masu Karatu a Sashen Kididdiga a Kwalejin, kuma ya rasu ne sakamakon raunin da ya samu bayan ’yan bindigar sun harbe shi.
- Matan Birnin Gwari sun amince maza su doke su
- Shekau ya zabi a yi masa azaba a lahira —Shugaban ISWAP
Marigayi Ahmad wanda ke ajin karshe na karatun Babbar Difloma, ya gamu da ajalinsa ne a hanyarsa ta dawowa dakin kwanansa tare da abokan karatunsa daga unguwar Gobirawa da ke daura da kwalejin.
A nan ne suka yi gamo da ’yan bindigar suna tsaka da kai hari a rukunin gidajen manyan ma’aikatan kwalejin.
Abokin dakin kwanansa, Hamza Abubakar, ya bayyana kaduwa tare da cewa Ahmad, “Mutumin kirki ne kuma ina jin dadin zama da shi a daki guda; Hakika an yi babban rashi.”
Hamza ya ce sun ji muryar marigayi Ahmad a lokacin da yake neman a kawo masa dauki, amma tsoro ya sa aka kasa fitowa a kai masa agaji.
A ranar Alhamis da misalin karfe 10:30 na dare ne ’yan bindiga suka kutsa Kwalejin, wanda mallakin Gwamnatin Jihar Kaduna ne, suka yi awon gaba da dalibai da ba a kai ga tantance yawansu ba.
Garkuwa a manyan makarantun Kaduna
Harin shi ne akalla irinsa na biyu a kwalejin na Nuhu Bamalli, daya daga cikin manyan makarantu hudu a Jihar Kaduna da ’yan bindiga suka kai hari tare da yin garkuwa da mutane.
Kafin shi, ’yan bindiga sun kutsa Jami’ar Greenfield da ke jihar, a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, suka yi garkuwa da dalibai da ma’aikata.
Masu garkuwar sun kashe biyar cikin daliban kafin daga baya suka sako ragoywar.
Gabanin harin Jami’ar Greenfield, ’yan bindiga sun kai hari a Kwalejin Gandun Daji na Gwamnatin Tarayya da ke garin Kaduna, suka yi awon gaba da dalibai 39.
Da kyar daliban suka shaki iskar ’yanci bayan iyayensu sun biya kudin fansa; Kodayake dalibi daya ya tsere daga hannun masu garkuwar.
A lokuta daban-daban, masu garkuwa sun kutsa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, suka sace mutane, ba su sako su ba sai da aka biya kudin fansa.
Jihar Kaduna ta yi kaurin suna wurin harin ’yan bindiga a manyan makarantu domin karbar kudin fansa.
Takaddamar biyan kudin fansa
Gwamnatin Jihar ta sha nanata cewa ba za ta tattauna da ’yan bindiga ba, ballantana ta biya su kudin fansa.
Ta kuma yi barazanar hukunta duk wanda ta gano ya tattauna ko ya biya su kudin fansa da sunanta.
Mutane da dama, musamman iyalan wadanda aka garkuwa yi gakurwa da su, na ganin matakin da gwamnatin ta dauka ya yi tsauri da yawa.
Amma masu ra’ayi irin nata suna ganin biyan kudaden fansa kara wa ’yan bindiga karfi ne da kuma samar musu kudaden sayen makamai su ci gaba da tafka ta’asar.