✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Ƙungiyar Afenifere, Adebanjo ya rasu

Ya rasu a safiyar yau Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke Lekki, a Legas Nijeriya yana da shekara 96.

Shugaban Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Pa Ayodele Adebanjo ya rasu yana da shekara 96.

Rahotanni sun ce dattijon ya rasu ne da safiyar Juma’a a gidansa da ke Lekki a Jihar Legas. An tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da iyalansa suka fitar.

“Ya rasu a safiyar yau Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke Lekki, a Legas Nijeriya yana da shekara 96. Za mu ci gaba da riƙe alƙawarinsa na fafutukar tabbatar da gaskiya da adalci.

Sanarwar ta ƙara da cewa, har zuwa ƙarshen rayuwarsa ya yi ta bayyana halayansa da gwagwarmayar na tabbatar da samun ’yanci da ci gaban Najeriya gaba ɗaya.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannu a madadin iyalan Madam Ayotunde Atteh (nee Ayo-Adebanjo), Madam Adeola Azeez (nee Ayo-Adebanjo), da Mista Obafemi Ayo-Adebanjo.

Shahararren Lauya, tsohon sakataren Ƙungiyar Action Group kuma shugaban Ƙungiyar Afenifere na Ƙasa, Adebanjo ya rasu ya bar matarsa, Cif Christy Ayo-Adebanjo da ’ya’ya, jikoki da ’ya’yan jikoki.