Shugaban China Xi Jinping ya samu damar ci gaba da mulki a wa’adi na 3 a Juma’ar nan, abin da ya maishe shi shugaba mafi karfin iko a kasar a cikin tsara da kakanni.
Wannan nadi da Majalisar Dokokin kasar ta yi wa Xi na zuwa ne bayan da ya samu karin wani wa’adi na shekaru 5 a matsayin shugaban jam’iyyar kwaminisanci a watan Oktoban shekarar da ta gabata.
- Wata Sabuwa: Dabdalar da ta wakana a Kannywood a makon jiya
- Kotun Koli ta ba wa Rufai Hanga na NNPP kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya
Bayanai sun ce wakilai kusan dubu uku suka amince da nadin Mista Xi a Majalisar Dokokin kasar kuma babu wani da ya nuna adawa da nadin nasa.
A wannan Juma’a, wakilan jam’iyyar suka zabe shi don yin wa’adi na 3, suka kuma sake nada shi a matsayin babban kwamandan rundunar sojin kasar.
An kawata dandalin Tiananmen da darduma ta kawa, da kuma allunan da ke nuna zabe mai muhimmanci da aka wa shugaba Xi, ga kuma makadan rundunar sojin kasar suna nishadantar da mahalarta dandalin.
Biyo bayan sanarwar sake bai wa Xi wa’adi na 3, wakilan jam’iyyar kwaminisanci sun sha rantsuwar nuna mubaya’a tare da kare kundin tsarin mulkin China.
Jim kadan bayan haka ne hugaba Xi ya sha rantsuwar kama aiki, daga nan ya sha alwashin ci gaba da gina China tare da karfafa tsarin tafiyar da al’amuranta.