✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Erdogan ya ayyana sake lashe zaben Turkiyya

’Yan adawa sun so kawo karshen mulkin Erdogan na tsawon shekaru 20.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ayyana lashe zaben shugaban kasar da a karon farko a tarihin ta aka kai ga zagaye na biyu.

Erdogan ya shaida wa dandazon magoya bayan sa cewar, zai kara jajircewa wajen rike amanar kasar a shekaru biyar da zai ci gaba da jagoranci.

Shugaban na Turkiya ya samu mafi rinjayen kuri’u a zaben da sama da kashi 52 na kuri’un da aka kada, yayin da abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu ya samu sama da kashi 47.

A lokacin da yake ayyana nasararsa a gaban magoya bayansa a wannan Lahadin, Shugaba Erdogan da yake rike da madafun ikon Turkiyya na tsawon shekaru fiye da 20, ya mika godiyarsa ga daukacin al’ummar kasar.

Sai dai har yanzu Kiliçdaroglu bai fito ya kalubalanci sakamakon zaben ba, ko da yake ana sa rai jagoran adawar kasar ya yi jawabi nan gaba kadan.

Tuni dai wasu shugabannin kasashen duniya suka fara tura sakon taya murnarsu ga shugaban.

Sarkin Katar Tamim bin Hamad Al Thani ya wallafa sakon taya murnarsa ga shugaba Erdogan a shafinsa na Twitter.

Kawo yanzu dai ba a sanar da nasarar ta shugaba Erdogan a hukumance ba.

Recep Tayyip Erdogan ya sha suka daga wajen ‘yan adawa, har ta kai ga sun kulla alaka tsakanin wasu jam’iyyu don mara wa Kemal Kilicdaroglu baya wanda ya zo na biyu a zaben don kawar da jagorancin Erdogan na tsawon shekaru 20.