✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin tsari da makabartun Kano ke fama da shi

Kowa yana diban wurin da ya yi masa a makabarta ya binne dan uwansa ba tare da yin layi-layi ba.

Makabarta ita ce gida na karshe ga kowane mutum, sai dai za a iya cewa makabartun Jihar Kano suna cikin wani hali na rashin tsari.

Wannan ya hada da rashin kula da mafi yawan makabartun suke fuskanta na zaizayewar kaburbura musamman a lokacin damina.

Baya ga yawan makabartun ta yadda za a ga kusan kowace unguwa tana da makabartarta, a gefe guda kuma makabartun suna nan kara-zube babu wani cikakken tsari na tafiyar da su.

Idan ka zagaya makabartun musamman wadanda ke cikin kwaryar Birnin Kano da suka hada da Makabartar Dandolo da ta Bulukiya da ta Sagagi da ta Abbatuwa da ta Hajikam da ta Tarauni da ta Tudun Murtala da ta Sauna da sauransu, za ka ga yadda mutane suke binne mamata ba tsari.

Kowa yana diban wurin da ya yi masa ya binne dan uwansa ba tare da yin layi-layi ba.

Maimakon a ce sai layin da aka fara ya cika sannan a sake bin wani layin, sai ka ga wannan layin bai cika ba amma an fara binnewa a wani layin na daban.

Baya ga wannan kuma a lokuta da dama a makabartun za ka ga yadda wasu suke da katange wasu kaburbura ko a yi musu rumfa, a wasu wuraren kuwa za ka tarar har sa tayil ake yi a jikin wasu.

Binciken da Aminiya ta yi ta gano cewa makabartun ba su da wani tsari na dauka tare da adana bayanan adadin mamatan da ake binnewa a cikinsu kamar yadda ake samu a wasu jihohi.

Malan Yusuf Tukur Tarauni shi ne Kakakin Kwamitin Kula da Makabartun Jihar Kano wanda Sarkin Fadar Kano Alhaji Ado Kurawa ke shugabanta, ya shaida wa Aminiya cewa babbar matsalar da suke fuskanta ita ce yadda mutane ke karya tsarin makabartun.

“Abin da ke damunmu shi ne yadda al’umma ba su ba mu hadin kai a duk lokacin da suka zo binne ’yan uwansu.

“A cikin kwamitinmu akwai ma’aikaci daga Ma’aikatar Kasa da Safiyo wanda yake aunawa tare da fitar da layi-layi a makabartun, amma sai ki tarar layin farko bai cika ba wasu su fara binnewa a layi na gaba.

“Ma’aikatanmu suna fama da al’umma a kan haka wallahi har fada ake yi tsakanin ’yan uwan mamaci da ma’aikatanmu.

“Ko kuma ki ga wasu mutane sun kwashi babban wuri da zai isa a binne mutum uku zuwa sama amma sai su yi amfani da shi a matsayin kabari daya. Su ma muna fama da tasu matsalar.

“Haka akwai wadanda suke binne ’yan uwansu ko malamansu sannan a yi wa kabarin rumfar kwano. Wannan ba daidai ba ne.

“Shi ya sa a yanzu muke hada kai da kafafen watsa labarai muna wayar wa jama’a kai game da yadda ya kamata su rika mu’amala da makabartu da sauransu,” in ji shi.

Sai dai ya ce hakkin daukar bayanan mamatan da ake binnewa a makabartu lamari ne da ya shafi hukumomin lafiya a kananan hukumomi.

“’A ka’idar aiki karamar hukuma ke da alhakin ajiye jami’in lafiya a makabarta wanda aikinsa shi ne daukar bayanan mamatan da suka rasu ana ajiyewa inda mu kuma daga wurinsu muke samun bayanai. Sai dai yanzu ban san dalilin da ya sa suka daina haka ba.

“Abin da zan iya tunawa shi ne lokacin da aka yi annobar Kwarona da aka samu mutane suka rika mutuwa to an ajiye jami’an lafiya da suke daukar bayanan mutane da ake binnewa a makabartun a kullum don taimaka musu su gano yawan mutanen da suke mutuwa.

“ Amma tun daga wancan lokaci ba su sake komawa makabarun ba,” in ji shi.

Alhaji Yusuf Tarauni ya ce “Muna zagaya makabartun domin mu gano halin da suke ciki, mu tattauna da ma’aikatan wurin don sanin korafe-korafen jama’a a kan makabartun tare da lalubo hanyar warware matsalolin.”

Ya ce a kwana nan Shugaban Kwamitin Sarkin Fardar Kano ya halarci kasar Masar don gano irin tsarin da suke gudanar da makabartunsu.

Sai ya yi kira ga al’umma cewa ya kamata a rika kai ziyara makabartu don sanin halin da suke ciki don ganin yadda za a tallafa musu.

“Kamar irin wannan lokaci da damina ke kawo jiki ya kamata a ce an yi gyara a makabartun. Kuma akwai bukatar kasa a makabartun duba da yadda ake samun mamakon ruwan sama da ke huda kabari.

‘Makabartu sun yi kadan’

Ya yi kira ga gwamnati ta kara yawan makabaru a jihar duba da cewa wadanda ake da su a yanzu sun cike yayin da kalilan daga cikinsu ke gab da cika.

“Mun dade muna sanar da gwamnati cewa makabartun da ke cikin birni sun cika, ana bukatar karin wurare.

“Mun rubuta wa gwamnati cewa ya kamata a fita daga wajen Kano kamar hanyoyinWudil da ta Dambatta da sauransu.

“Idan kin duba za ki ga cewa a mota ake zuwa makabartu don haka babu wani batun nisa da sauransu.”

“Kwamitin ya yi kira ga gwamnati ta mayar da kwamitin zuwa wata hukuma tsayayya wacce doka za ta kafa ta.

“Idan har wannan kwamiti ya tashi daga matsayin kwamiti zuwa hukuma wacce doka ta kafa ta, duk yayin da kwamitin ya sa wata doka to za a samu mutane sun yi biyayya tare da kiyayewa saboda sun san cewa hukuma ce mai doka wacce idan aka samu wanda ya keta dokokin hukumar za ta iya gurfanar da shi gaban kotu.

“Haka idan aka samu hukuma za a ware mata kudi don gudanar da ayyukanta,” in ji shi.

Har ila yau ya koka kan yadda mutane ke yin makabartu a unguwanninsu ba tare da sanar da hukuma ba, Ya ce, “Wani abin da ke faruwa shi ne yadda wasu ke yin makabarta ba tare da neman izinin hukuma ba.

“Misali wani mai hali sai ya bayar da filinsa don a yi makabarta a unguwa. Ya kamata idan aka yi haka a sanar da hukuma don a samu kwararu kan muhalli su bincika su ga shin kasar wurin ta dace da makabarta ko a’a.

“Wani lokacin kuma za ki tarar bayan ya bayar da filin nasa an yi makabarta idan ya ga unguwar ta zama maraya sai ya karbe ya gina gida a kai.

“Bayan akwai ka’ida sai makabarata ta shekara 40 sannan za a iya yin amfani da ita a matsayin wani ginin daban, amma a irin wadannan unguwanni wata makabarta ba ta fin shekara 15, amma za ki ga an gine ta.”

‘Yadda muke fama da mutane’

Wani daga cikin masu aiki a Makabartar Tarauni wanda ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa suna fama da mutanen da ke dagewa cewa sai sun binne ’yan uwansu a wani rukuni daban.

“Mutane suna da wata dabi’a wai sai sun ware rukunin iyalinsu daban a makabarta. Za ki ga mutane sun zo sun ce sai a wurin da aka binne kakanninsu da iyayensu za su binne sauran iyalinsu.

“Wani lokaci kuma ko babu isasshen wuri, to haka za su dage sai su kwafa su binne a wurin,” in ji shi.