Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zabi Festus Keyamo (SAN) domin ya zamo mai magana da yawunsa a bangaren yakin nema zabensa na 2019.
Lauyan ya tabbatar da zabensa da aka yi a shafinsa na twitter, inda ya ce, “An zabi in zama Daraktar tsare-tsare da yada labarai wato mai magana da yawun yakin neman zaben Shugaban Kasa na 2019. Zan yi jawabi na musamman nan bad a jimawa ba.”
Takardar da aka aike masa wadda ke sanar da shi wannan matsayi, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi wanda kuma shi ne shugaban kungiyar yakin neman zaben Buhari ne ya sanya wa hannu.