✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Buhari ya yi fatan ya sake tsayawa takara

“Da farko ina neman afuwarku, kasancewar na zaunar da ku har wani tsawon lokaci. Haka ya faru saboda na dage akan gwamnonin da suke halartar…

“Da farko ina neman afuwarku, kasancewar na zaunar da ku har wani tsawon lokaci. Haka ya faru saboda na dage akan gwamnonin da suke halartar wannan taro. Shi ya sa na taho da su mu sadu da ku tare, ta yadda idan kun koma kun sadu da sauran ‘yan Najeriya, ku fada musu cewa gwamnoninsu na cikin ‘yan rakiyar shugaban kasa. Ina jin haka zai kara mani kuri’a a nan gaba. Na yi matukar farin ciki da suka samu halarta.” 

Wadannan kalamai, da suke jurwaye mai kamar wanka, na cikin irin kalaman da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya furta a lokacin da ya samu ganawa da shugabannin al`ummomin `yan kasar nan mazauna kasar Kodebuwa, a lokacin da ya ke ganawa da su a Abijan babban birnin kasar a yammacin ranar Talata 28-11-17, kasar da ya ziyarta   don halartar taron hadin gwiwa karo na 5, na kungiyar Tarayyar Afirka wato AU da na Tarayyar Turai wato EU. Kalaman da  yanzu suke ‘yar manuniya ga ‘yan kasar nan da ma na duniya baki daya akan Shugaba Buhari yana fatan zai sake neman takarar neman mukamin shugabancin kasar nan a inuwar jam’iyyarsu ta APC a shekarar babban zaben kasar nan na shekarar 2019.

Furucin da ‘yan kasa musamman ‘yan siyasa na jam’iyyarsa ta APC da ma na sauran jam’iyyun adawa suka dade suna jira. Kafin wadancan kalamai gwamnoni da kungiyoyi da wasu daidaukun `yan kasa da dama sun sha yin kiraye-kirayen lallai sai Shugaba Buhari ya amsa kiraye-kirayen da suke yi masa. A takice ka iya cewa wasu ma sun fara yi masa yakin neman zabe, alal misali kamar hadaddiyar kungiyar nan ta magoya bayansa da ke karkashin jagorancin mashawarcinsa na musamman akan harkokin siyasa Mista Giedom Sammani, tuni suka fara yi masa yakin neman zabe, inda suke bin shiyyoyin kasar nan suna yekuwar ayyukan da Shugaba Buhari ya aiwatar a karkashin jam`iyyarsu ta APC. 

Kamar yadda gamayyar kungiyoyin suke fada, ayyukan sun hada da bashin noman shinkafa da ciyar da daliban makarantun Firamare Karin kumallon safe da na samar da ayyukan yi ga matasa na N-Power da na bayar da bashi mai saukin ruwa ga masu kananan sana`o`I da makamantansu. Ko a makon da ya gabata gamayyar wadannan kungiyoyi sun kai wannan gangami a shiyyar Arewa ta tsakiya a garin Lafiya babban  birnin jihar Nassarwa. Shi kansa Minista Yada labarai kuma Kakakin gwamnatin tarayya Alhaji Lai mohsammed ya dade da yana jagorancin wasu Ministoci daga jiha zuwa jiha, inda sukan shirya kalankuwa don fadakar da mutanen jihar, inda Gwamnatin APC ta Shugaba Buhari ta sa gaba wajen cikasa alkawurran da ta yi wa jama`a a lokacin yakin neman zaben shekarar 2015, da suka danganci inganta matakan tsaro, musamman a jihohin shiyyar Arewa maso Gabas da rikicin `yan kungiyar Bioko Haram ya daidaita da farfado da tattalin arzikin kasar nan da sauran makamantan matsaloli.

Ba ko shakka matsananciyar rashin lafiyar da Shugaba Buhari ya sha fama da ita da ta haddasa masa doguwar jinya tsakanin bara da bana, ita ta rinka jefa fargaba da shakku a zukatan wasu `yan jam`iyyarsa ta APC da ma magoya bayansa da sauran `yan kasa tsammanin cewa Shugaba Buhari ko kusa ba zai kammala wa`adinsa na zangon farkon nan ba, wato zuwa 29 ga watan Mayun 2019, balle ma ya ce zai sake neman tsayawa takara a shekarar 2019. Hakan ta sa wasu daga cikin gwamnonin jam`iyyarsu ta APC na Arewacin kasar nan musamman na shiyyar Arewa maso Yamma da suka fito daga shiyya daya da Shugaba Buhari wasunsu suka rinka kai gwauro suna kai mari da fatan idan har ta Allah ta kasance, kamar yadda ta kasance a kan marigayi shugaban kasa Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa, wato Shugaba Buhari ya mutu, to su a ba su mukamin mataimakin shugaban kasa. Wasu daga cikin irin wadancan gwamnoni ne yanzu kuma da su ka ga shugaba Buhari ya murmure suka kuma dawo su ne kan gaba sai Shugaba Buhari ya sake neman tsayawa takara.

Tun da yanzu Shugaba Buhari ya yi wancan furuci da masu fatan ayyukan alherin da ya fara su ke jira na zai sa ke tsayawa zabe, don cigaba da ayyukan da za su cigaba da ceto ‘yan kasa daga mummunan mawuyacin halin kuncin rayuwa da suka samu kansu a ciki, a zamanin gwamnatin da ta gabata, kamar yaki da cin hanci da rashawa, ta hanyar kwato makudan biliyoyin kudade da kaddarori daga  wadanda suka sace su, suka jibge a gida da kasashen waje da kuma irin yadda gwamnatinsa ta tashi tsaye haikan tana ta kokarin kawo karshen rikicin `yan kungiyar Boko Haram da farfado da tattalin arzikin kasar nan, tattalin arzikin kasar da tun a karshen watannin shiddan farkon wannan shekarar, masana tattalin arziki da Hukumar kididdiga ta kasa suka sanar da duniya cewa ya fita daga tabarbarewar da ya fada, yanzu ma a karshen watanni taran wannan shekarar wadancan Hukumomi dai sun sake bada tabbacin cewa tattalin arzikin ya nunka daga bunkasar kashi 0.70, zuwa kashi 1.40 cikin 100.

Duk da wadannan aikace-aikace da kuma begen da jama’a suke akwai babban kalubale tare da Shugaba Buhari a kan sake neman takararsa, amma ba daga mafi yawan talakawan kasa ba masu kada kuri’a, ‘a ‘a sai dai daga cikin jiga-jigan jam’iyyarsa ta APC, da kuma daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP. Alal misali a kwanakin baya, gwamnoni da ‘yan majalisun Dokoki na kasa da na jihohi da dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na shiyyar Kudu masu Yamma, sun yi wani taro a Badun, inda suka bayyana matsayinsu cewa, ‘babu tikitin kai tsaye ga shugaba Buhari,’ wannan wani abin dubawa ne idan aka yi la’akari da irin yadda shiyyar take siyasa a dunkule da kuma irin yadda wancan shiyya ta bada gagarumar gudunmuwar da ta kai Shugaba Buhari samun nasarar zaben 2015. 

Yadda shugabancin jam’iyyarsa na kasa da wasu gwamnonin jihohi suke kokawa da ba su samun kulawar Shugaba Buhari wajen tafiya da su a cikin gwamnatinsa, kodayake a ‘yan kwanakin nan ya amince wa shugabancin jam’iyya na kasa da gwamnoninsa da su fito masa da sunayen wasu ministoci da yake son sake nadawa a majalisar zartawar kasar nan. Rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin bangaren zartarwa da majalisun Dokoki na kasa, musamman majalisar Dattawa duk wasu abubuwa ne da ya kamata Shugaba Buharin ya fara aniyyar yadda zai magance su. 

Duk da yake babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta daura damara wajen kawo karshen rikicin da ta afka tun bayan da ta fadi zabubbukan 2015, inda a gobe Asabar in Allah Ya kaimu take babban taronta na kasa don zaben sababbin shugabanni, da kuma irin yadda tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da ya bar jam’iyyar kusan shekaru 4 da suka gabata zuwa APC yanzu ya yi wa jam’iyyar kome, kuma ana sa ran ya nemi takarar mukamin shugabancin kasar nan. 

Mai karatu idan ka tattara wadannan kalubale da na iya ambata da ma wadanda ba ambata ba za ka ga cewa, Shugaba Buhari yana da babban aiki gabansa, amma inda aikin yake mai sauki shi ne yadda har gobe talaka mai kada kuri’a yake tare da shi. Allah ya bada sa’a.