Shugaban Kas Muhammadu Buhari ya gana da malaman jami’a su uku da wasu mata su goma da aka ceto daga hannun Boko Haram.
Shugaban ya gana da su ne a yau Litinin a fadar Shugaban Kasa da ke gidan gwamnati a Abuja.
A lokacin taron ganawar, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara nanata qudurinsa na kubuto da sauran wadanda ke hannun ‘yan Boko Haram din.