✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na sane da halin da ake ciki —Minista

Sanin matsalolin Najeriya da rashin aikin matasa ne ya sa Shugaba Buhari bullo da shirye-shiryen tallafa wa mutane da abun dogaro da kai. Ministan Harkokin…

Sanin matsalolin Najeriya da rashin aikin matasa ne ya sa Shugaba Buhari bullo da shirye-shiryen tallafa wa mutane da abun dogaro da kai.

Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Muhammad Maigari Dingyadi ya sanar da haka a bayaninsa kan umarnin Shugaban Kasa ga kowane minista ya koma jiharsa ya yi wa al’umma bayanin halin da ake ciki da hanyoyin magance rikicin kasa.

Dingyadi ya ce Buhari ya yi alkawalin biyan bukatun masu zanga-zangar #EndSARS, tare da kara albashin ’yan sanda da sauran jami’an tsaro.

Ya kara da cewa a shirye shugaban yake ya gyara aikin tsarin aikin dan sanda domin nasara nasara da sabon sauyi a rundunar.

Ministan ya ce gwamnati ta yi imani cewa bata-gari sun shiga cikin zanga-zangar #EndSARS, suka tayar da rikici da sace-sace wanda ya ce gwamnati ba za ta lamunta ba.