Sanin matsalolin Najeriya da rashin aikin matasa ne ya sa Shugaba Buhari bullo da shirye-shiryen tallafa wa mutane da abun dogaro da kai.
Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Muhammad Maigari Dingyadi ya sanar da haka a bayaninsa kan umarnin Shugaban Kasa ga kowane minista ya koma jiharsa ya yi wa al’umma bayanin halin da ake ciki da hanyoyin magance rikicin kasa.
- Matakin da ya kamata Buhari ya dauka kan zanga-zangar #EndSARS
- An ci gaba da fasa rumbun adana kayan abinci a Abuja
- Kwamitin binciken cin zalin ‘yan sanda zai fara zamansa a Legas
- #EndSARS: ‘Yan sanda sun cafke mutum 55 a Kano
Dingyadi ya ce Buhari ya yi alkawalin biyan bukatun masu zanga-zangar #EndSARS, tare da kara albashin ’yan sanda da sauran jami’an tsaro.
Ya kara da cewa a shirye shugaban yake ya gyara aikin tsarin aikin dan sanda domin nasara nasara da sabon sauyi a rundunar.
Ministan ya ce gwamnati ta yi imani cewa bata-gari sun shiga cikin zanga-zangar #EndSARS, suka tayar da rikici da sace-sace wanda ya ce gwamnati ba za ta lamunta ba.