✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shirye-shiryen Sallah: Taskun da coronavirus ta jefa ’yan kasuwa

A bisa al’ada, yayin da Musulmi a fadin duniya ke ban-kwana da watan Ramadana sukan fara shirye-shiryen bukuwan Idul Fitri, wanda aka fi sani da…

A bisa al’ada, yayin da Musulmi a fadin duniya ke ban-kwana da watan Ramadana sukan fara shirye-shiryen bukuwan Idul Fitri, wanda aka fi sani da Karamar Sallah.

A bana dai an samu sabani a Najeriya, inda wasu suka yi nasu bikin Sallar ranar Asabar, wasu kuma ke yi ranar Lahadi. Wasu ma sun riga sun yi tun ranar Juma’a.

Sai dai shirye-shiryen Sallar na bana ba su yi armashi ba saboda annobar COVID-19, wadda ta tilasta wa hukumomi daukar matakan dakile yaduwarta, ciki har da jingine Sallar Idi, da hana bukukuwa a wuraren taruwar jama’a, da sauran su.

Yayin da miliyoyin wasu mutane ke zaman gida, wasu kuma aljihunsu ba nauyi, Aminiya ta ziyarci kasuwar Kado da ke Abuja, Babban Birnin Tarayya, da jajibirin Sallar don ganin wainar da ake toyawa.

Yayin da ta dauki matakan ba da tazara kamar yadda hukumomi da masana harkar kiwon lafiya ke ba da shawara, wakiliyarmu ta tattauna da wasu ’yan kasuwa.

Lamarin sai du’a’i

Surajo Umar wani mai sayar da tufafi ne da ya koka da halin da aka shiga.

“Mutane na neman na abinci ne ba na sayen tufafi ba, don haka ba ciniki bana idan kika kwatanta da bara.

“Bara kasuwa ta yi kyau – galibin mutanen da suka zo suka sayi kaya a bana suna korafin cewa ya zama musu dole ne saboda yara na kuka suna bukatar kayan sallah”, inji shi.

”Yan kasuwa sun koka da rashin ciniki bana, musamman idan aka kwatanta da bara

Da ta matsa bangaren da ake sayar da kayan lambu kuma, wakiliyarmu ta tattauna da Ibrahim Umar, wani mai sayar da tumatiri da ya ce babu kasuwa duk da cewa tumatir da dangoginsa na cikin kayan da girki ba zai hadu ba idan babu su.

Muna godiya ga Allah, akwai ciniki daidai gwargwado bana, amma ba za a taba kwatanta shi da bara ba”, inji Malam Ibrahim.

Zamanin coronavirus

Shi kuwa Malam Aminu Abubakar mai sayar da kayan kwalliya cewa ya yi game da kasuwar bana:

“Muna zamanin coronavirus, mutane ba sa saye. Duk matan da ke zuwa shagona sayen kayan kwalliya an tilasta su zaman gida saboda wannan annoba.

“Yanzu kyallen rufe fuska ake saya a maimakon jambaki, lamarin sai la haula wa la kuwwata.

“Amma bara, kasuwa ta yi kyau, kudi ya shigo sosai. A ko wanne hali dai muna yi wa Allah godiya”.

Duk da sun yi ciniki daidai gwargwargwado, masu sayar da kayan abinci ma sun ce lamarin sa du’a’i

Da wakiliyarmu ta nemi jin ta-bakin Nura Umar, daya daga cikin mutanen da suka je sayayya a kasuwar, sai da ya yi ajiyar zuciya sannan ya furta kalmar hakuri!

“Lamarin sai hakuri, babu tufafin da na saya saboda babu kudi. Dokar zaman gida ta sa na kashe duk abin da na tara dole, don ba zan zauna da yunwa ba.

“Ranar Sallah zama na zan yi a gida na ci abin da ya sawwaka.

“Wannan ba lokaci ne na shagulgula ba, lokaci ne da ya kamata mu yi amfani da damar da wata mai tsarki ya ba mu, mu yi addu’o’in allah Ya kawo mana dauki”.

‘Dole a rage sanwa’

Ita ma Amina Idris, wata baiwar Allah mai ‘ya’ya hudu, ta je kasuwar ne da nufin yin cefanen Sallah, amma tashin farashin kaya ya shammace ta.

“Kasafin da na yi don wannan cefanen N9,000 ne, amma saboda farashin kaya ya tashi, dole sai na rage abincin sallar da zan girka wa iyalina.

“Ina addu’a Allah Ya kawo karshen wannan annoba kafin ta yi tasiri a kan sauran bangarorin rayuwa”, inji ta.

Bana dai wannan Sallah ta zo da takura ga mutane da dama, ko dai ta fuskar karancin kudi, ko ta ciniki, ko ma ta walwala.