Edita ka ba ni dama na yi tsokaci, dangane da soma aiki da kashin farko na matasa da suka kammala karatu za suyi a shirin Npower. Hakika ko shakka babu fitar da jerin sunayen matasa dubu 200, da gwamnatin tarayya ta yi daga cikin dubu 500 da za ta samar wa da ayukka a shirin Npower, dukkan alamu sun nuna cewa kwalliya za ta biya kudin sabulu, duba da yadda mafi akasarin wadanda suka samu nasara a shirin ‘ya’yan talakawa ne, da suka nema ta hanyar yanar gizo, wanda da ba ta wannan hanyar ba ce, sai dai ‘ya’yan talaka su rika gani ga masu uwa a gindin murhu.
Da wannan nake kira, ga dukkanin shuwagabannin shirin, da su aiwatar da tantancewa ta zahiri, bisa gaskiya da adalci ba tare da sanya son rai a ciki ba, tare da tura dukkanin wadanda sukayi nasara a makarantun da ke bukatar kwararrun malamai, musamman ma makarantun firamari da ke yankunan karkara. Haka zalika akwai bukatar gwamnati, ta soma shirin fitar da jerin sunayen kashi na biyu na shirin, domin matasan da sukayi rijistar shirin suga sunyi bankwana da zaman kashe wando, a sakamakon rashin ayukkan yi. Daga Kwamred Aminu Dankaduna Amanawa, 07065654787
Godiya Ga Jaridar Aminiya
Tabbas jaridar Aminiya kin cancanci yabo duba da irin gagarimin gudumuwa da kike ba mu wajen bayyana ra’ayoyoyinmu mabanbanta, Daga karshe na ke muku fatan alheri da kuma gamawa lafiya. Daga Sani Mohammed Chindo. Unguwar karofin madaki a Bauchi, 08030918913
A yi kyakkyawan tsari ga ’yan gudun hijirar Arewa maso Gabas
Gasiya, ya kamata gwamnatin Najeriya, ta yi wani kyakkyawan tsari na kula da ’yan gudun hijirar arewa maso gabas, saboda a zahiri ’yan gudun hijirar suna fama da wahala, idan mutun yaga yadda ’yan gudun hijirar suke bi kwararo-kwararo suna bara, gaskiya akwai tausayi idan mutun yaga irin halin da ’yan gudun hijiran suke ciki, saboda taimakon da ake aika musu baya shiga hannunsu kamar yadda ya kamata. Saboda, haka ya kamata gwamnati ta sa mutanen da ta yadda da su, masu mahimmanci da gaskiya da rokon amana, wadanda za su iya aikin tallafawa ’yan gudun hijirar yadda ya kamata, wadanda za basu duk wani abun da da aka bayar saboda su. Daga Muhammad Babangida Kiraji, Gashua, 08029388699
Zuwa ga jama’ar Ghana
Al’ummar kasar Ghana Allah ya sa ku zabi abin da zai zamo muku Alkhairi ga kasarku da ma Duniya baki daya, Allah ya raba ku da yin da na sani. Daga Salisu Armaya’u Nguru,Jahar Yobe Najeriya.08069383959, 08022567450, [email protected]
Ga Gwamnan jihar Zamfara
Assalamu alaikum Aminiya Hausa, da fatar ma’aikatan ku na cikin koshin lafiya, yau ina so ku bani dama, Kamar yadda kuka saba inyi kira ga gwamnan jihar Zamfara, wato Abdul-aziz Yari Abubakar, a kan dan Allah ya Taimaka ya biya kudin Jarabawar Waec da Neco ta shekarar 2016, da kuma jarabawar Neco ta 2015, domin daliban nan su samu damar zuwa makarantar gaba da sakandare, babu shakka yanzu wadannan yaran suna nan suna yawo a tituna ba tare da sanin makomar su ba, ilmi dai gishirin zama duniya ne. Daga Ibrahim Rabilu Tsafe jahar Zamfara, 07064282182
Gaisuwa ga ma’aikatan Aminiya
Salam Edita da fatan kana cikin koshin lafiya, dan Allah ka bani dama in isar da skon gaisuwa tag a ma’aikatan jaridar Aminiya mai albarka. Da fatan kowa na cikin koshin lafiya. Allah kuma ya kara daukaka jaridar Aminiya mai farin jinni. Daga Hon. Shamsu Muh’d Katsina, 07039878892
Kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi
Ya kamata su lura da wajen samar da iri da injuna duk na zamani, kamar wajen sarrafa shinkafa da kuma takin noma. Domin shine kadai mafita a wannan halin da ake ciki. Aminiya ina muku fatan alheri. Daga Uba Ahmed Balarabe K.D, 07037775159
Zuwa ga Gwamna Ganduje
Salam Edita, ka mika min sakona zuwa ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje da a taimakemu a gyara mana hanyar mu wacce Kwankwaso ya fara saura kadan y agama, Allah bai bashi iko ba. Mai girma gwamna a dube mu da idon rahama a karasa mana dan yanzu tsakanin tashar baduku da rogo da damina, ba karamar wahala ake sha ba. Daga na ku Yakubu Abdullahi fulatan karamar hukumar Rogo, jihar Kano, 07035224185/080986868993
Allah jikan Ado Bayero
Allah ka jikan mai martaba sarkin Kano Alhaji Dokta Ado Bayero. Shugaba Muhammadu Buhari dan Allah a sa kujerar sarautar Kano a siyasa duk mai so ya tsaya takara tin da Sunusi ya shiga siyasa ya fita daga uban kasa. Daga Muh’d Salees mai Arsenal Kanan Dabo, 08068693974
Zuwa ga Buba Galadima
Aminiya ‘yar amana, dan Allah ku mika min sakona ga injiniya Buba Galadima da yake cewa idan Buhari bai sa baki ba a rikicin APC, a 2019 wai zai rasa jam’iyyar da zai tsaya takara. To ka sani mu talakawa ko da jam’iyya ko ba jam’iyya za mu zabi Buhari domin mu ba jam’iyya b ace a gaban mu, Buhari shine a gaban mu. Daga Musa Unguwar mai yasin, danja jihar Katsina, 08060611124