A lokacin da nake gudanar da nazari kan tatsuniya da kagaggun labarai a matsayin dalibar Digiri na Biyu (Digiri na Biyu kan Adabi) a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ne na fara haduwa da Hajiya Iyatu Abba, wata fitacciyar ma’aikaciya a gidan rediyon Jihar Bauchi (BRC) da ake ji a jihar da jihohin makwabta sakamakon yadda takware wajen sarrafa harshe don gabatar da shirinta na “Kunnenka Nawa.”
Shirin ‘Kunneka Nawa’ shiri ne da ake karanto littattafan kagaggun labarai da ake kira da ‘Littattafan Adabin Kasuwar Kano’ a gidan rediyon Bauchi. Garuruwan jihohin makwabta kamar Gombe da Filato da Kaduna da Kano da Jigawa da sauransu sukan saurari shirin a lokacin da suka kama matsakaicin zango (MW) da tashar kade-kade (FM) na gidan rediyon Jihar Bauchi.
A yayin da take gabatar da shirin a matsakaicin zango (MW) jihohi da dama na sha’awar shirin nata idan aka lura da dimbin wasikun yabo da na bayar da gudunmawa da ake samu daga jihohin. Hakika Hajiya Iyatu Abba ta cancanci yabo a wannan gidan rediyo bisa kokarinta na ci gaba da gudanar da wannan shiri na karanto kagaggun labarai (na kusa ko fiye da shekara 20). Kuma duk da cewa shiri ne na karanto littattafan kagaggun labarai, yadda Hajiya Iyatu Abba ke sarrafa harshe wajen karanto littattafan shi kansa abin a yaba mata ne.
Wadannan littattafan Adabin Kasuwar Kano littattafai ne da aka rubuta su da Hausa kuma sun jawo hankalin masu fashin baki da masu suka. Kuma mafi yawancin masu sukarsu suna da yakinin cewa littattafan sun taimaka wajen yaduwar rashin tarbiyya a tsakanin al’umma, don haka ba su dace da al’adun Hausawa da al’umma ba. Sai dai a wannan bangare ne fasahar sarrafa harshe da kwarewar Hajiya Iyatu Abba suka taka rawa.
Wadannan kagaggun littattafai da ake karantawa a gidan rediyon kai ka ce ba wadanda jama’a ke karantawa ba ne, tamkar ta haddace su ne kafin ta karanto. Yadda take karanta su tana kokarin kiyaye al’adar bayar da labari na gargajiya da kwarewarta wajen bayar da labarin da ja hankalin masu saurare su kasance tare da ita abin yao ne. Takan yi amfani da muryarta wajen nuna yadda halayen taurarin cikin littattafan suke. A wannan lokaci tana sarrafa muryarta ta yi sama ko kasa, domin ta jawo hankalin masu saurare kan wani abu mai daga hankali da ke faruwa. A lokacin da muryarta ta daga sama tana nuna wa masu saurare ne cewa mai maganar yana cikin fushi ko zargi ko kuma damuwa.
Wani muhimmin al’amari shi ne Hajiya Iyatu Abba takan cire kalmar da take ganin cin zarafi ne ko ba ta dace da al’adar Hausawa ba, ko kuma rashin girmamawa ce a wurin masu saurare, saboda bayani da baki na iya jawo matsala ga al’umma. Don haka Hajiya Iyatu ke canja wadannan kalmomi ko ta cire su saboda kwarewar da take da ita a harshen Hausa. Domin masu saurarenta ba sun takaita ga wani rukuni na mutane ba ne, a’a, manyan ’yan boko da shugabannin addini da na siyasa da jahilai da yara da sauransu duk suna sha’awar shirin saboda ana gabatar da shi cikin saukakkar Hausa. Kuma kwarewarta ya mayar da ita wata mai shiga tsakani ta hanyar gidan rediyon, inda take zama gada a tsakanin marubuta littattafan da masu saurare, wanda hakan ke samar da wata kafa ta musayar ra’ayi. Misali a bayan an kammala karanta littafi a rediyo akan gabatar da wasu tambayoyi kamar:
Mene ne fahimtarka a kan littafin?
Me yake karantarwa?
Me ka karu da shi, fadakarwa ko karantarwa?
Wadannan tambayoyi na iya zama jigon batu ko manufa ko fahimtar mutum kan wani littafi. Abin mamaki akan samu daruruwan rubutun zube kan wadannan tambayoyi da aka yi.
Wadannan amsoshi ana yin maki dinsu ne a karkashin wani kwamiti da gidan rediyon na Bauchi ya kafa kuma a bayar da kyauta a kansu.
A wani bangare, Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi Hajiya A’isha Yuguda tana amfani da wannan dama wajen wayar da kai a fannin rayuwa da siyasa tare da bayar da wasu kyaututtuka ga masu sauraro. Sanya hannun matar Gwamnan ya nuna yadda masu sauraro suke jin dadin wannan shiri. A yanzu da tsarin bayar da labaran baka na gargajiya (tsatsuniya da almara) ke bacewa, kafafen labarai masu aiki da lantarki (musamman rediyo) na ci gaba da kasancewa wajen bayyanawa da adana adabin baka.
Muna iya cewa Hajiya Iyatu ta samu nasarar zama wata fasihar mai bayar da irin wadannan labarai, domin bayar da labari ba ya tsaya a kan labarin kawai ba ne, a’a hade yake da rayayyen labari, halin da ake ciki, murya, amon muryar, ajiye magana, bayyana jin dadi ko damuwa a yayin bayar da labarin da kuma irin yadda za a sanya masu saurare su rika tsokaci. Simms: (1982).
Akporobaro: (2005) ya kara da cewa kawata magana wajen bayar da labari ya kunshi abubuwa uku da ba a raba su; jawo hankalin masu saurare da ci gaba da rike masu sauraren da kuma isar wa masu sauraren kwarewar da ake da ita. Hajiya Iyatu duk tana cimma wadannan abubuwa uku. Kuma galibin masu sauraren Hajiya Iyatu mata ne, bisa lura da yawan wasikun da ake samu daga gare su kan shirin.
Manufar karanta kagaggun labarai irin wadannan ita ce; labaran tare da sauran fannonin al’adu na jama’a su hadu su gina wata ingantacciyar rayuwa da tabbatar tasirinta. Wannan na nufin tun da al’umma ta kunshi bangarori da dama, to gudanar da wadannan bangarori na da muhimmanci domin a ji dadin gudanar da ita al’ummar gaba dayanta, ke nan zaman kan da sassan suke yi wani muhimmin abin lura ne wajen nazarin gudanuwarsu.
Daga abin da ya gabata, yadda nazari ke gudana yana tafiya ne tare da rawar marubuci da kafar sadar da rubutun da masu saurare suke takawa a kokarinsu na inganta rayuwar al’umma. dimbin sakonnin marubuci ana iya sanya su a salo-salon da za su samu hanyar isa ga jama’a ta hanyar karanta kagaggun labaran. Masu sauraren da ba za su iya karantawa ko sayen wadannan littattafai, suna iya saurare ta gidan rediyo. Sauraren wadannan kagaggun labarai ta rediyo kan ba su damar sanin sakon marubuta. Don haka za a iya cewa, wadannan kagaggun labarai manyan hanyoyi ne na fadakarwa da nishadantarwa da suke karfafa ilimi da fahimta da imani da dabi’un mutane. Kuma suna koyar da yara abin da yake daidai da tunatar da manya wasu dabi’u da al’umma ta amince da su.
Don haka yana da kyau an kafa wata cibiya ta masu karanta kagaggun labarai da bayar da tasuniyoyi. Kwatankwacin kungiyar Bayar da Labaran Tatsuniyoyi (National Storytelling Network – NSN) ta Amurka da Society of Storytelling ta Ingila.
Bincike na baya-bayan nan ya nuna galibin wadannan labarai an mayar da su fina-finai musamman a Kano.
Hajiya Iyatu Abba ta taka rawar gani a kokarinta na jan hankali da ci gaba da rike masu saurarenta. Kuma tare da taimakon gidan rediyon da masana za a iya kafa wata cibiya ta hada masrubuta da masu saurare.
Jinjina ga Hajiya Iyatu Abba kan wannan aikin yabo.
Manta Adamu
Email: [email protected]