✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin kawar da Buhari: Gangamin Obasanjo bai gangamu ba

Naja’atu ta ce ba ta san maganar ba Ba a gayyace ni ba – Balarabe Musa An kaddamar da wata kungiyar gangami da tsohon Shugaban…

Naja’atu ta ce ba ta san maganar ba

Ba a gayyace ni ba – Balarabe Musa

An kaddamar da wata kungiyar gangami da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bukaci a kafa don kawar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben badi, kasa da mako daya da caccakar da ya yi wa Shugaba Buhari da manyan jam’iyyun kasar nan, wato APC da PDP.

kungiyar mai suna Gangamin Yunkurin (Najeriya For Nigeria Mobement- CNM), an kaddamar da ita ce a shekaranjiya Laraba a Cibiyar Shehu Yar’aduwa da ke Abuja, sai dai kuma ga dukan alamu gangamin bai gangamu ba, ganin ’yan kalilan din mutane ne suka halarta, yayin da wadansu da aka sanya sunansu, suka ce ba su san maganar ba, ko ma an sanya sunayensu ne ba tare da an sanar da su ba.

Masu shirya gangamin sun musanta cewa suna yi wa Obasanjo aiki ne, inda suka ce yunkurin nasu wani kokarinsu ne na kashin kai domin kai Najeriya tudun mun-tsira.

In za a iya tunawa a wani “Bayani na Musamman” zuwa ga Shugaba Buhari a makon jiya mai taken: “Mafita: Yekuwa don samun Gangamin Yunkurin Najeriya” Cif Obasanjo ya bukaci Buhari da kada ya tsaya takara a karo na biyu, inda ya zargi Shugaban da gazawa da kuma nuna kabilanci.

Taron gangamin na shekaranjiya an sa ran zai tattaro manyan ’yan siyasa da suka hada da gwamnoni da wakilan Majalisar Wakilai da Sanatoci masu ci.

Sai dai, ba ma su ba, fuskokin da aka gani a wurin gangamin ba su taka kara sun karya ba. An dai samu tsofaffin gwamnoni biyu ne kacal da suka hada da Olagunsoye Oyinlola na Jihar Osun da Donald Duke na Kuros Riba, sai kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP, Kanar Ahmadu Ali (mai ritaya) da wasu kalilan din ’yan siyasa.

Shi kansa Cif Obasanjo bai halarci gangamin ba, sai dai Kakakinsa Kehinde Akinyemi ya ce tsohon Shugaban kasar ya dawo ne  daga Addis Ababa ta kasar Habasha inda ya halarci taron Tarayya Afirka a makare. A jiya Alhamis Obasanjo ya yi rajista da kungiyar ta CNM a Cibiyar ’Yan jarida da ke  Abeokuta, inda ya ce sun kafa kungiyar ce domin ganin an mayar da ragamar mulkin kasar nan hannun matasa. 

A taron na Abuja dai an ga daruruwan matasa sanye da riguna da hulunan da suke dauke da tambarin kungiyar gangamin mamaye da wurin taron kuma rike da tutoci da kyallaye da kuma fosta-fostarta, wasu masu alamar taswirar Najeriya da hannu biyu dauke da ita.

A wurin taron abokan siyasar tsohon Shugaban kasar sun ce Gangamin Najeriya an shirya shi ne domin kawar da gwamnatin APC a shekarar 2019 ta hanyar samar da mafita mafi dacewa.

Da yake jawabin bude gangamin, tsohon Gwamnan Jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola wanda shi ne Mukaddashin Shugaban Gangamin ya bayyana kungiyar da “wani yunkuri da ya dauki nauyin ceto Najeriya daga mummunan shugabanci.”

Oyinlola, wanda ya taba zama Sakataren Jam’iyyar PDP ta kasa, ya ce Najeriya ta tunkari rugujewa har sai da Cif Obasanjo ya farkar da kowa daga gyangyadin da yake yi.

Ya ce, ‘Bayani na Musamman’ na Obasanjo ya jawo aka samar da zabi na uku.

A cewarsa, gangamin zai bayar da dama daidai-wa-daida ga ’yan Najeriya musamman mata da matasa, ta yadda za su yi amfani da basirarsu yadda ta kamata.

Sai dai Oyinlola, ya yi watsi da zargin da wadansu ke yi cewa, gangamin wani yunkuri ne da Obasanjo ke yi domin ya kwace harkokin siyasar kasar nan bayan ya riga ya yi ritaya daga siyasar jam’iyya.

 “A ce muna halatta tsare-tsaren Obasanjo ba gaskiya ba ne. Babu wanda zai soki batutuwan da Obasanjo ya tado a wasikarsa. Kada ku damu da dan sako mu tattauna sakon. Abin da ya yi ya farkar da mu daga barcin da muke yi mu fahimci hakikanin abin da ke faruwa a Najeriya, sannan mu dauki mataki a kai,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Shin babu wadansu shugabanni ne da suke raye kuma suke ganin yadda abubuwa suke gudana? Ina jin ya kamata mu yaba masa a kan yadda ya fadakar da ’yan Najeriya kan cututtukan al’umma da suke bukatar a magance su.” 

Tsohon Gwamnan ya kuma bayyana niyyarsa ta sauka daga mukamin Shugaban Hukumar Gudanarwar Hukumar Katin dan kasa (NIMC) domin samun nasarar wannan gangami ta CNM.

“Wannan aiki ne na wucin-gadi a hukumar da ke nufin zan halarci taro sau hudu kawai a shekara. Na shiga jam’iyyar siyasa ce domin in bauta wa kasata, kuma aikina a Hukumar NIMC shi ma na kasata da mutanen kasata ce. A yanzu dai mu ba jam’iyyar siyasa ba ce,  kuma mun san cewa a karkashin tsarin mulki, za ka iya tsayawa takara ce kawai a karkashin wata jam’iyyar siyasa.”

A nasa jawabin, tsohon Gwamnan Kuros Riba, Cif Donald Duke wanda ke cikin masu kiran taron, ya ce gangamin ya samu gagarumar karbuwa tun bayan gabatar da shi, inda ya ce, “wahalar da ake ciki” a kasar nan tana faruwa ce sakamakon dogon lokacn da aka dauka ana mummunan mulki.

“Muna da masu magana a kowane sashi na kasar nan, a kowace mazabar Sanata. Za su koma gida su isar da abubuwan da muka tattauna a nan. Idan muka samu dandazon jama’a masu yi da gaske, to za ta iya komawa jam’iyyar siyasa, amma in ba za mu samu haka ba, to za mu gusa zuwa mataki na gaba.

Wani dan Kwamitin Dattawan Jam’iyyar APC, Alhaji Buba Galadima ma ya bayyana goyon bayansa ga gangamin, inda ya ce, bai saba ka’idar kasancewarsa dan jam’iyya mai mulki ba.

“Ba jam’iyyar siyasa ba ce; wani gangami ne da aka hadu domin ceto kasarmu,” inji shi.

Game da ko zai goyi bayan sake zaben Shugaba Buhari a badi, Buba Galadima ya ce,”Idan Shugaban kasar yana so a sake zabensa, to, sai ya nuna mana cikakkun hujjoji na cewa ya taka rawar gani wajen samar da kayayyakin bunkasa kasar nan, ko ya samar da abinci cikin sauki ga jama’a, ko ya yi kokarin dinke kasar nan; in ya yi haka ne za mu shirya don sake zabensa, amma