✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin hidimar kasa (NYSC), a ci gaba ko a soke shi?

A `yan kwanakinnan wasu kafofin yada labarai sun ta kawo labaran cancanta da rashin cancantar a ci gaba da shirin yi wa kasa hidima, wato…

A `yan kwanakinnan wasu kafofin yada labarai sun ta kawo labaran cancanta da rashin cancantar a ci gaba da shirin yi wa kasa hidima, wato NYSC, koma a soke shi kwata-kwata kowa ya huta, bisa ga irin yadda suke ganin shirin tamfar yana neman shiriricewa, bayan samun shekaru 43, da kirkirowa, shirin da gwamnatin mulkin soja ta tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ta kirkiro, bisa ga tanadin Dokar soja da ake yi wa lakabi da dokar dikiri (decree) mai lamba 27, ta ranar 22-05-1973, daga bisani kuma wata dokar ta soja mai lamba 51, ta ranar 16-06-1993, bayan shekaru 20, cif-cif da fara shirin ta yi masa kwaskwarima. 

kirkiro shirin ‘NYSC,’ a wancan lokaci, bai rasa nasaba da irin yadda gwamnatin ta dukufa a kan wasu manyan shirye-shirye guda uku da suka hada da sake ginin kasa da sasanta `yan kasa da tsugunnarwa, bayan kammala yakin basasar watanni 30 da kasar nan ta yi fama da shi tsakanin shekarar 1967 zuwa farkon 1970. Ma`ana, ta kowace fuska a samu yadda za a sake farfado da kasar nan walau a kan fannin tattalin arzikin kasa ko na zamantakewa cikin hanzari bisa ga irin tabo da koma bayan da yakin basasar ya jaza wa al`ummarta baki daya.
A wancan lokaci, an fara shirin na NYSC da dukkan matasan kasar nan da suka samu kammala karatunsu na Digiri ko na babbar takardar shaidar Difloma ta kasa, wato HND, ko wadanda suka kammala takardar shaidar Malanta mai daraja ta daya wato NCE, walau a cikin kasar nan ko daga kasashen waje. An rinka tura irin wadannan matasa zuwa jihohin da ba na haihuwarsu ba, wato akasarin matasan jihohin Arewa a kan tura su Kudanci, na jihohin Kudu, kuma su zo jihohin Arewa. Duk dai don a kara samun hadin kai da famintar juna ta fannin bambance-bambancen al`adu da addini da jinsi da ma na zamantakewar al`ummomi daban-daban, ta yadda fahimta da girmama juna za su kara samuwa, kuma su ginu a tsakankanin matasan kasar baki daya, wadanda su ne manyan gobe.
Daga bisani da tafiya ta yi tafiya, an tsame matasan da suka kammala ilmin NCE, aka bar masu digiri da HND, wadanda har ya zuwa wannan lokaci da su ake bugawa. Sai dai kuma a baya-bayannan an tsame dukkan matasan da suka haura wa shekaru 30, haihuwa daga cikin shirin na NYSC, sabanin farkon fara shirin da ake yi da kowa da kowa. Ana zargin an yi haka ne, bisa ga zargin ko dai matsalar wadatattun kudi ko kuma yawa da masu hidimar kasar suka fara yi, bisa ga karuwar al`umma da yawaitar jami`o`i da manyan makarantu a kasar nan.
Ta wannan shiri na NYSC. Matasa da dama na kasar nan musamman na jihohin Arewa da akasari wasunsu suka kasance kifin rijiya, ma`ana an haife su a garuruwansu, inda a nan suka taso suka kuma yi dukkan karatuttukansu, har zuwa jami`a ko wata babbar Kwaleji. bullo da shirin ‘NYSC,’ ya ba su damar zuwa jihohin da ba su taba tunanin za su je ba, bare kuma har su share shekara guda suna cudanya da mutanen yankunan da aka tura su. Hakan ya rinka bayar da damar kara samun hadin kai da fahimtar juna akan bambance-bambancen al`adu da addini, kamar dai yadda shahararren mawakin Hausannan marigayi dan Anache Gandi yake cewa a cikin wata wakarsa “Na zaune bai ga gari ba, sai gari ya ganai.”
Dadin-dadawa shirin na NYSC, ya kara taimaka wa mutanen Arewa wajen `yan Kudu su kara fahimtar `ya`yan masu kora shanu, kamar yadda wasu `yan Kudun suke kiran `yan Arewan a kan ba su yin karatun zamani, cewa batun ba haka ba ne, bisa ga irin matasa masu kananan shekaru da ke shiga cikin shirin, kuma su ga sun san abin da suke a kan fannin ilmin da suka karanta.
A takaicen takaitawa shirin na NYSC, shiri ne da aka bullo da shi da aniyar ya kara dankon zumunci da cusa kaunar juna da kishin kasa da sadaukar da kai don taimaka wa `yan kasa a kan ci gabansu da ma kasar baki daya, wanda kawo yanzu ka iya cewa, ba tare da wata fargaba ba, shirin ya cimma wadannan manufofi, duk kuwa da irin yadda wasu suke kallon bai cimma wadancan manufofi ba.
Masu irin wancan ra`ayi na gazawar shirn na NYSC na kafa hujja da irin yadda suke ganin fitintuna irin na tashe-tashen hankula da sukurucewar matakan tsaro a dukkan sassan kasa, wadanda suka hada da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa satar shanu da rikicin Fulani makiyaya da manoma da `yan shekarunnan ya dauki wani sabon salo da rigingimun siyasa masu kama da addini da fasa bututun man fetur a `yankin Neja Delta mai arzikin man fetur da yunkurin tabbatar da samar da kasar Biyafara a shiyyar Kudu maso Gabas da rikicin `yan kungiyar Ahlis Sunnah Lid-Da`await Wal jihad da ake yi wa lakabi da Boko Haram da ake fama da ita yau sama da shekaru 6, a shiyyar Arewa maso Gabas da ta watsu cikin kasa da matsalar tattalin arzikin kasa da ta jaza rashin ayyukan yi, musamman ga matasan kasar nan da dai sauran matsaloli.
Tabbas wadannan matsaloli da makamantansu akwai su a cikin kasar nan, amma abin da nike so mai karatu ya fahimta ba shirin NYSC, ya kawo su ba. Don kuwa zai yi matukar wahala ga matashin da ya samu ilmi, har zuwa matsayin Digiri ko HND, ya mayar da kansa dan tada husuma da fadace-fadace a cikin kasa, har sai da samun daurin gindin shugabanninsa, musamman na siyasa, wadanda akasarinsu ba su samu yin wani karatu mai zurfi ba.
A ra`ayina soke shirin na NYSC, ko kadan ba shi zai magance koke-koken da ake da shirin ba. Kamata ya yi mahukunta su yi kwaskwarima a kan yadda ake tura matasan jihohin da suke aiwatar da shirin, ta hanyar kyautata jin dadin rayuwarsu, da koya musu sana`o`in dogaro da kai, da sama musu jarin da za su rinka fuskantar sana`o`in da suka koya a lokacin shirin, da uwa uba bullo da darussan cusa kishin kasa da kaunarta da mutanenta tun daga makarantun Firamare zuwa na Sakandare da na gaba da Sakandare da ma cikin sannsanin daukar horon sanin makamar shirin na NYSC.
Su kuma iyaye da shugabannin wannan zamani da ma masu zuwa nan gaba, ya kamata su rinka sa tsoron Allah a cikin zukatansu, ta hanyar gabatar da shugabanci a kan abin da ya ba su cikin kamanta gaskiya da adalci, ba tare da neman shugabancin ba a zaman ko a mutu, ko a yi rai, kamar yadda ake fama yanzu. A ra`ayina har a yau, har gobe shirin na NYSC yana da gagarumar gudummuwar da zai bayar cikin samun hadin kai da ci gaban kasar nan da al`ummarta, don haka batun a soke shi a ganina bai ma taso ba.