Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno, ya ce Shirin Afuwa ga Tsagerun Neja Delta na shugaban kasa (PAP), ya lakume Naira biliyan 712 da aka kasa bayani kanta.
Monguno ya fadi haka ne a ranar Juma’a yayin da ya ke magana da ’yan jarida bayan tattaunawarsu da shugaba Muhammadu Buhari kan shirin, a fadarsa da ke Abuja.
- Rashawa: Babu Gawuna a binciken da muke yi -Muhuyi
- Buhari ya nada Dokio shugaban shirin afuwa na Neja Delta
Baya ga Shugaba Buhari da Monguno a zaman tattaunawar, akwai shugaban shirin na PAP, Kanar Milland Dixon Dokio mai ritaya.
Monguno ya ce, an nada sabon mukaddashin mai gudanar da shirin afuwar don ya dakile rashawar da ta yi wa shirin dabaibayi.
Ya ce: “Abun mamaki, abubuwa da yawa sun faru.”
Kamar yadda Kanar Dixion ya ce, “akwai rashawa da almubazzaranci a tsawon lokacin da aka kwashe, an lalata naira biliyan 712, da ba a iya bayanin yadda aka kashe ta ba.”
“A takaice, wannan matsananciyar rashawar da ta lalata shirin afuwar kuma ta sanya mutanen Neja Delta cikin kuncin rayuwa wanda dole ne a yi maganinta cikin gaggawa.”
Dokio ya bayyana cewa akwai rashin gaskiya da rashawa wajen bayar da kwangiloli da samar da kayayyaki a shirin.
Ya ce, “bisa wannan dalilin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa shirin garam bawul domin ya kasance wadanda aka yi shirin don su suna amfana.”