A yau, ina so ne mu soma koyarwa game da wannan kan magana wanda na ce da ita – SHIRI DOMIN GAMUWA DA ALLAH – Wannan yana da muhimmanci ga kowane dan Adam musamman a wannan zamanin da muke ciki. Sau da dama mutane sukan manta cewa, a wannan duniya, babu wanda zai dauwama, dukanmu dan lokaci kadan ne muke da shi; amma babbar damuwar ita ce; yawancin lokaci, mutum yakan manta cewa rana tana zuwa wadda dole ne mu fuskanci Ubangiji Allah da kanSa; yaya muke shirin saduwa da Allah idan lokaci ya yi? Rayuwar da muke yi yanzu ne irin shiri da muke yi har ran da za mu sadu da Ubangiji Allah.
A cikin Littafin Ruya ta Yohanna 20: 11 – 15, maganar Allah na cewa “Na ga kuma babban farin kursiyyi da wanda ke zaune a bisansa, wanda duniya da sama suka guje ma fuskatasa; ba a kuwa samu musu wuri ba. Na ga matattu kuma, kanana da manya, suna tsaye a gaban kursiyyin; aka bude littattafai; aka bude wani littafi kuma, Littafin Rai ke nan: aka yi wa matattu shari’a kuma bisa ga abin da aka rubuta cikin littattafai, gwargwadon ayyukansu. Teku kuma ya ba da matattun da ke cikinsa; mutuwa da Hades kuma suka ba da matattun da ke cikinsu: aka yi musu shari’a kuma, kowane mutum gwargwadon ayyukansa. Kuma aka jefar da mutuwa da Hades cikin korama ta wuta, Mutuwa ta biyu ke nan, wato korama ta wuta. Kuma wanda aka iske ba a rubuta shi cikin littafin rai ba, aka jefar da shi cikin korama ta wuta.”
Zu mu yi bincike a wannan wurin da muka karanta, bari mu sake karatu daga cikin Littafi Mai tsarki – 2Korinthiyawa 5: 1 – 11, “Gama mun sani idan wannan gidan nan, wurin zaman jikinmu na duniya ya rushe, muna da gini daga wurin Allah, gidan da ba a yi da hannuwa ba, madauwami ne, cikin sammai. Gama hakika cikin wannan muna nishi, muna marmari mu samu sutura da mazauninmu wanda ke daga sama; domin da samun sutura, kada a iske mu da tsiraici ba. Gama hakika mu da ke cikin wannan mazaunin jiki muna nishi, mun nawaita; ba cewa muna so a kware mana sutura ba, amma a kara bisanta, domin abin da ke na mutuwa, rai shi hadiye. Shi fa wanda ya gudana mu zuwa wannan, Allah ne, Wanda Ya ba mu shigambiyar Ruhu. Da shi ke fa kullum muna da karfin zuciya, muna kuwa sane muddar muna nan zaune cikin jiki, a rabe muke da Ubangiji. (gama bisa ga ban-gaskiya muke tafiya, ba bisa ga gani ba) muna da karfin zuciya, na ce, mun fi so kuma mu kasance a rabe da jiki, muna zaune tare da Ubangiji. Domin wannan fa anniyarmu ke nan, ko a zaune ko a rabe, mu zama masu gamshe shi. Gama dole dukanmu za mu bayyana a gaban dakalin shari’a na Kiristi; domin kowane daya ya karbi sakamakon aikin da ya yi cikin jiki ko nagari ko mugu. Da shi ke fa mun san tsoron Ubangiji, muna rinjayar mutane, amma mu mun bayyana ga Allah; ina kuwa sa zuciya mun zama bayyanannu cikin lamirai naku.”
Ashe akwai ranar tsayuwa gaban Allah Madaukakin Sarki, a wancan rana ba za ka iya guje wa fuskar Allah ba, babu wurin buya, a yadda kake ko kike; haka za mu bayyana a gabanSa; mu da kanmu daidai za mu zo mu ba da lissafin kanmu game da abubuwan da muka yi yayin da muke rayuwa cikin duniya. A lokacin babu asiri, komai zai bayyana a fili; ko abubuwa masu kyau ko marasa kyau. Mutum bai isa ya boye wani abu daga fuskar Allah ba. Zan so in soma da shari’ar masu Bin Yesu Kiristi:
DAKALIN SHARI’A NA KIRISTI: Sai mu san wannan sosai, cewa shari’ar da za a yi a dakalin shari’ na Kiristi, shari’ar masu bin Yesu Kiristi ke nan; a wurin ne za a duba irin aikin da muka yi yayin da muke cikin duniya a matsayinmu na masu bi, yadda muka yi aikin da kuma nufin zuciyarmu yayin da muke yin aikin. A cikin Littafin 1Korinthiyaywa 3 : 9 – 21 maganar Allah tana cewa “Gama mu abokan aiki na Allah ne, ku kuwa gonar Allah ne, ginin Allah ne. Ni kuwa, bisa ga alherin Allah da aka ba ni, kamar magini mai gwaninta na kafa gindi, wani kuwa yana tada gini a kai. Amma kowane mutum ya yi hankali irin ginin da yake yi a kai. Gama ba wanda yana da iko ya kafa wani gindi daban da wanda an rigaya an kafa ba, Yesu Kiristi ke nan. Amma idan kowane mutum ya yi gini bisa gindin nan, ko zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ingirci, ko tattaka, aikin kowane mutum za ya bayyanu: gama ranar nan za a tone shi, da yake cikin wuta za a gwada ta; wuta kuwa da kanta za ta gwada aikin kowane mutum, na kowane iri ne. Idan aikin kowa da ya gina a kai ya tsaya, za ya karbi lada. Idan aikin kowa ya kone, za ya sha hasara, amma shi da kansa za ya tsira; amma sai ka ce ta wurin tsakiyar wuta. Ba ku sani ba ku haikali ne na Allah, Ruhun Allah kuwa a cikinku yake zaune? Idan kowa ya bata haikalin Allah, Allah za Ya bata shi, gama haikalin Allah Mai tsarki ne, wato ku ne. Kada kowa ya yaudari kansa. Idan kowane yana tsammani shi mai hikima ne a cikinku cikin wannan zamani, bari ya koma wawa domin ya zama mai hikima. Gama hikimar wannan duniya wauta ce ga Allah. Gama an rubuta, shi wanda yakan kama masu hikima da nasu wayo: da kuma, Ubangiji Ya san tunanin masu hikima, wofi suke. Domin wannan kada kowa ya yi fahariya a kan mutane. Gama dukan abu naku ne.”
Ina so mu gane wani abu sosai game da rayuwar da muke yi a cikin wannan duniya, duk abin da muke yi, maganar Allah ta kwatanta shi da gini, wannan ya kunshi aikinmu na yau da kullum, ya kunshi aikin ibada da muke yi. Mu san wannan sosai cewa abin da yake cikin zurfin tunanin mutum a bayyane yake a gaban Allah. Dukkan nufin zuciyar mutum a fili yake a gaban Allah. Mu sani fa, babu wanda zai dauwama a cikin duniyar nan, dukanmu kamar kasuwa muka zo ci, idan an tashi dole ne mu koma gida. Wani irin shiri ne muke yi domin mu sadu da Ubangiji? Wace irin rayuwa kake yi a yau wadda za ta ba ka tabbaci cikin zuciyarka cewa a shirye kake; ko da mutuwa za ta zo yanzun nan, ba za ka ce da na sani ba?
Bari mu kasance tare mako mai zuwa idan Allah Mai iko duka Ya bar mu cikin masu rai. Kada mu manta yin addu’a domin shugabaninnmu na kasa da na jihohi da kananan hukumomi. Allah Ya taimake mu, amin.