✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben shugabannin PDP ya raba kan Tambuwal da Bafarawa

Zaben shugabannin jam’iyar PDP da za a gudanar a matakin kananan hukumomi dana jiha, na ranakun 5 ga watan Satumbar 2020 da kuma 12 ga…

Zaben shugabannin jam’iyar PDP da za a gudanar a matakin kananan hukumomi dana jiha, na ranakun 5 ga watan Satumbar 2020 da kuma 12 ga wata ya raba kan Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa, kan bukatar da kowannensu na jagorantar jam’iyar a matakin jiha.

Jagororin sun yi ta kokarin boye wannan bambanci tun kafin bayyanar lamarin a gaban magoya bayansu a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar da aka gudanar a gidan gwamnati a ranar Litinin da ta gabata, wanda hakan ne ya sa ake zargin uwar jam’iya ta dage zaben har ta nada wasu shugabannin jam’iyar a jiha su jagoranci gudanar da jam’iyar kafin zabe bayan wa’adin da aka kara wa shugabannin a matsayin rikon kwarya ya kare, saboda samar da maslaha da sulhu.

Bayanan da Aminiya ta samu sun ce Bafarawa ya amayar da abin da ke damunsa a tafiyar da jam’iya kamar yadda shi ma Gwamna Tambuwal ya yi a gaban masu ruwa da tsaki na jam’iyar a Sakkwato.

“Gaskiya an kai matsayar za’a zo a zauna a sulhunta a nada kwamiti a kowace karamar hukuma a duba yanda za’a shigowa da kowa don a yi adalci.

“In wannan silhun ya tabbbata an yi adalci an yi yadda jama’a suke so to ba matsala”, A cewar wata majiya mai goyon bayan bangaren Bafarawa.

Majiyar ta ci gaba da cewa “jagororinmu a jiha (Tambuwal da Bafarwa) kawunansu ya rabu, lalle jagorori cikin bayanansu an samu matsaloli amma mun so a fito da wani tsari wanda ya kamata shugabannin su yi tun farko.

“Ka san wanda yake babba koyaushe tunaninsa daban ne da na dan karami don ba ruwansa da wahala, mun so a kasa mukaman nan bangaren wane da wane.

“Sai ga shi kawai aka ce an kafa kwamiti a kananan hukumomi su je su yi aiki. Mun yarda su yi aiki amma a gyara kwamitin domin ’yan bagare biyu ne kawai aka sanya don ba mu son a samu matsala.

“Maganar kashi ba ta taso ba, tsohon labari ne ba mu aminta da shi ba don mu muka zabi gwamnati, a lokacin da za ka yi mana maganar kaso a lokacin da gwamna ya zo da mutanensa ba mu zabe sa ba; A yanzu ko mun kada masa kuri’a kamar kowa a jam’iya daya muke, sai dai mu yi kaso a raba daidai (50-50) tun da mun yi aiki.

“Mu bangaren Bafarawa muke shi ne jagoranmu duk abin da muka samu albarkacinsa ne, dole mu yi masa da’a duk sanda abin bacin rai ya same shi dole ranmu ya baci; In na jin dadi ne dole haka.

“Kai ka san ba a cewa Garkuwa bai iya wani abu a Sakkwato, ba gaskiya ba ne, duk wanda yake Sakkwato ya san yanda aka yi zaben gwamna na gaba daya da na cike gurbi (inconclusive) ko sanda Garkuwa yake gwamna bai sha wahala kamar lokacin zaben ba”, a cewarsa.

Daya daga cikin Kwamishinonin Tambuwal Muhammad S/Arewa a zantawarsa da wakilinmu ya ce, “fatarmu shugabannin nan su dawo kan tebur ina ba su shawara su dawo kan tebur su fito a fili su kasa shugabancin nan kowa ya dauki abin da zai dauka.

Ya ce a yi abin da zai sa a tafi da magoya bayan kowa kar a bar wasu baya.

Ya ce ko shi da yake mataimakin shugaban jam’iyya a yankin Sakkwato ta tsakiya kafin a nada shi kwamishina kuma yanzu aka sanya shi cikin kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar ba’a taba kiran sa ba; Duk tsare-tsaren da aka yi ba a ce masa komai ba, shi dai yana saurare ya ji abin da ake ciki, ‘amma ita uwar jam’iyya ta san da ni da matsayina’ inji shi.

Abdullahi Yusuf Hausawa dan kwamitin rikon kwarya na jam’iyar PDP a Sakkwato ya ce a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar an tsara kowace karamar hukuma za su zauna, kowane bangare ya nada wakilci sai su fito da mutanen da za su jagorance su, jam’iya za ta sanya ido yadda abubuwa za su tafiya, PDP daya ce ba zancen a bai wa wani kaso.

Ya ce “ko ku kuka zauna taro ana samun bambancin ra’ayi wannan ba komai ba ne don a karshe an tashi cikin raha da dariya”, inji Hausawa.