✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Naja’atu da Bafarawa sun kafa sabuwar tafiyar matasan Arewa 

Bafarawa ya ce, “Lokaci ya yi da matasa za su karɓi jagoranci. Idan aka ba su dama, za su taka rawar gani...

Fitacciyar ’yar gwagwarmayar Arewa, Hajiya Naja’atu Mohammed da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa sun kaɗɗamar da wata sabuwar tafiyar matasa domin ceto yankin Arewacin Nijeriya.

A ranar Talata ne manyan ’yan siyasan Arewan suka ƙaddamar da tafiyar matasan da nufin tallafa wa matasan Arewa da kuma lalubo mafita daga matsalolin siyasa da tattalin arziki da suka dabaibaye yankin.

A jawabinsa, Bafarawa wanda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar DPP ne, ya shaida wa mahalarta taron cewa, “lokaci ya yi da matasa za su karɓi jagoranci. Idan aka ba su dama, za su taka rawar gani, muddin suka samu gogaggun dattawa da ke ɗora su a kan hanya.”

Ya ce, ƙungiyar mai suna Northern Star Youth Movement Initiative (NSYMI) na shirin buɗe rassa da ofishin a faɗin yankin Arewa, domin ba wa matasa dama da kuma abubuwan da suke buƙata.

A nata ɓangaren, ɗaya shugabar tafiyar, Hajiya Naja’atu Mohammed, ta jaddada cewa ƙungiyar ba ta siyasa ba ce, ta mayar da hankali ne kawai wajen tallafa wa matasa da kuma kawo ci-gaban yankin Arewacin Najeriya.

“Manufarmu a fili take: amfani da ƙarfi da kuma basirar da Allah Ya yi wa kowane ɗan Arewa domin kawo ci-gaban rayuwa da na tattalin arziki a yankin,” in ji Hajiya Naja’atu.