✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace fasinjoji, sun ƙone mota a Zamfara

Harin na zuwa ne bayan Bello Turji ya yi barazanar kai sabbin hare-hare a sabuwar shekara.

’Yan bindiga sun kai wa wata mota ɗauke da fasinjoji hari a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara, inda suka sace dukkanin fasinjojin motar sannan suka ƙone motar.

Lamarin ya faru a garin Kwanar Jalab da ke gundumar Zungeru a safiyar ranar Talata.

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, “’Yan bindigar sun tare motar, suka sace fasinjoji goma, sannan suka ƙone motar.

“Wannan shi ne karo na farko da suka ƙone mota bayan sun yi garkuwa da mutane. Lamarin ya tayar da hankali sosai.”

Wannan hari ya haifar da fargaba ga masu tafiye-tafiye, inda mutane da dama suka dakatar da zirga-zirgarsu tsakanin Gusau da Shinkafi.

Sulaiman Shinkafi, wani mazaunin yankin, ya ce, “Mahaifiyata ta hana ni yin tafiya bayan ta ji labarin wannan abu.

“Muna zaton mutum 10 aka sace saboda yawanci irin wannan motar na ɗaukar mutane 10 ne.

“Muna fatan gwamnati za ta ɗauki mataki cikin gaggawa don hana ƙaruwar hare-hare.”

Harin na iya zama wani ɓangare na barazanar da Bello Turji ya yi, cewa zai kai farmaki idan ba a saki yaransa da jami’an tsaro suka kama ba.

Turji ya yi barazanar kai hare-hare a Zamfara da Sakkwato daga ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara idan ba a biya masa buƙatunsa ba.

Bafarawa ya buƙaci gwamnati ta ɗauki a kan Turji

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa a kan Turji.

“Gwamnati ta ɗauki barazanar Turji da muhimmanci kuma ta kare al’umma,” in ji Bafarawa.

“Muna buƙatar zaman lafiya don magance matsalolin yunwa da rashin aikin yi, amma dole ne a haɗa hannu don tallafa wa jami’an tsaro.”

A halin yanzu, sojoji sun bayyana Bello Turji a matsayin “wanda ya kusa zuwa hannu” tare da alƙawarin kawar da shi.

A cewar Manjo Janar Buba, “Sojoji suna ƙara matsa lamba a kan ‘yan ta’adda.

“Turji zai gamu da irin abin da shugabannin ’yan ta’adda da dama suka fuskanta a wannan shekarar.

“Sojoji sun ƙuduri aniyar kare ’yan Najeriya daga waɗannan bata-gari.”