Ya zuwa yanzu dai babu batun dawowar Shugaba Muhammadu Buhari Najeriya, bayan tafiyarsa ganin Likita a birnin Landan makonni biyu da suka gabata.
A ranar Talata, 30 ga watan Maris ne Shugaba Buhari ya tafi birnin Landan domin a duba lafiyarsa, inda Fadar Shugaban Kasa ta sanar cewa zai dawo ne a mako na biyu na watan Afrilu.
- Mutum dubu 100 sun tsere zuwa Nijar kan hare-haren Boko Haram a Borno
- Hisbah ta kama samari da ’yan mata marasa azumi a Kano
Sai dai Gwamnatin Tarayya a yanzu ta sanar cewa babu wani abin damuwa game da lokaci ko rashin dawowar shugaban kasar daga wannan balaguro da ya yi.
A yayin amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa a Fadar Shugaban Kasa, Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya gaza bayyana takaimaiman ranar dawowar shugaban kasar da a yanzu ya shafe tsawon kwanaki 15 a birnin Landan.
A cewar Ministan, “yau fa Laraba ce, kuma wannan mako zai kare ne a ranar Asabar, to kuma mene ne abin damuwa a nan?”
Bayan zaman Majalisar wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta, Lai Mohammed ya ce abin da suka fi mayar da hankali a yanzu shi ne kalubalen tsaro da ya addabi kasar.
Tafiyar da Shugaba Buhari ya yi ta zamto abin magana, inda wasu bangarori suka rika Allah wadai da kakkausar murya musamman yadda tafiyar ta zo a daidai lokacin da likitoci suka shiga yajin aiki.
Da dama daga cikin al’ummar Najeriya sun bayyana bacin ransu kan tafiiyar Buhari kasar Birtaniya domin a duba lafiyarsa.
Wasu sun kira hakan a matsayin barnatar da kudin talakawan kasar masu biyan haraji yayin da wasu kuma ke sukar gazawar gwamnatin na inganta harkokin kiwon lafiyar da suka tabarbare.
An yi wa Buhari zanga-zanga har kashi biyu a Landan
Wasu ’yan Najeriya mazauna kasar Birtaniya, sun yi wa Buhari zanga-zangar adawa a birnin Landan, inda suka nemi ya koma gida domin inganta harkokin kiwon lafiya a kasarsa.
’Yan Najeriyar dai sun rike kwalaye masu dauke da sakon kiran Shugaban da ya koma gida yayin da suka yi cincirindo a bakin Asibitin Wellington da kuma kofar gidan Gwamnati Najeriya da ke birnin Landan.
Bayan haka, wasu magoya bayan shugaba Buhari sun tattaru a gidan Gwamnatin Najeriya da ke Landan, inda suka jaddada goyon bayansu ga shugaban tare da yi masa addu’a da fatan alheri.
Magoya bayan nasa sun mamaye Kofar Gidan na Abuja House ne, rike da alluna da kwalaye masu dauke da sakon fatan alheri ga Najeriya gami da yabo da jinjina ga Shugaban Kasar.
‘Yaushe Boris Johnson zai zo Najeriya a duba lafiyarsa’
Da ya ke sharhi kan kalubalantar tafiyar da Buhari ya yi zuwa Landan, Sanata Dino Melaye, tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya yi tambayar “yaushe ne Firaiministan Ingila, Boris Johnson zai zo ziyarar duba lafiyarsa a Najeriya?”
Sai dai Fadar Shugaban Kasar ta mayar masa da martani da cewa, Buhari na da ’yancin tafiya duba lafiyarsa a ko’ina a fadin duniya, musamman idan aka yi la’akari da zaman jinyar da ya yi a baya.
Dalilin da Buhari bai mika wa Osinbajo mulki ba
Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Mallam Garba Shehu, ya bayyana dalilin da Shugaba Buhari bai mika wa mataimakinsa ragamar jagorancin kasar ba yayin tafiyarsa birnin Landan ganin likita.
Yayin wani shiri na siyasa da gidan Talabijin na Channels ya shirya, Mallam Garba ya ce kwanakin da Shugaban kasar zai dauka a wajen Najeriya kalilan ne da ba su kai ga ya mika wa Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo akalar jagorancin kasar ba.
Hadimin Shugaban Kasar ya ce ubangidansa bai karya wata doka ba don zai ci gaba da aiki daga duk inda ya kasance.
A cewarsa, “abin da doka ta tanada shi ne idan Shugaban Kasa zai kai kwana 21 ko fiye, to ya wajaba ya mika wa mataimakinsa mulki, amma a irin wannan yanayi bai kasance dole ba.”