A ’yan kwanakin nan an samu rade-radi masu yawa cewa ’yan sandan kasar nan za su tsunduma yajin aiki, a kan rashin aiwatar da karin albashi da alawus-alawus, al’amarin da ya tada hankalin al’umma, ganin cewa tuni malaman jami’a ke nasu yajin aikin, ga kuma barazanar ’yan bindiga da ke ta’azzara a yankuna daban-daban na kasar nan.
Idan za a iyatunawa, a bara ne Ministan Kula da Harkokin ’Yan Sanda Alhaji Muhammad Aliyu Dingyadi ya ce za a kaddamar da sabon tsarin albashi da alawus-alawus ga ’yan sanda a watan Janairun bana, amma dai har zuwa yanzu shiru ake ji, hakan bai faru ba.
- Yadda rashin wutar lantarki da karancin man fetur suka janyo cikas a Najeriya
- Rasha ta ci gaba da isar da iskar gas zuwa Turai —Gazprom
Sai dai kuma dangane da batun na yajin aiki, Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Alkali Usman Baba ya ce babu wani jami’in dan sanda da zai kuskure ta shiga wani abu wai shi yajin aiki, a kan rashin kaddamar da sabon tsarin albashi, domin sun san illar da ke tattareda yin hakan.
Usman na mayar da martani ne a kan wasu rahotanni da ake ta yadawa a kafofin yada labarai da ke cewa ’yan sandan suna shirin shiga yajin aiki a ranar 26 ga wannan wata, domin neman karin albashi da alawus-alawus.
A sanarwar da Sufeto-Janar din ya fitar, wacce mukaddashin mai magana da yawun Rundunar ’Yan sanda Muyiwa Adejobi ya fitar tana cewa, kowa ya san Rundunar ’Yan sandan kasar nan tana cike da da’a da girmama dokokin aiki, wadda kuma take da tsari na bin doka don magance duk wata takaddama, kuma tsarin yajin aiki ba ya cikin hakan.
“Sanin kowa ne cewa ’yan sandan kasar nan suna sane da cewar duk wani yunkuri na kowane irin jami’an tsaro don shiga shafi yajin aiki ko kuma makamancin haka, bai halasta ba gare su kuma ba abin amincewa ba ne, domin tsarin aikin shi ne ba da muhimmanci ga zaman lafiya da kuma tsaron kasa,” inji Sufeto Janar Baba.
Sai ya bayyana rahotan da ke cewa akwai shirin yin yajin aiki da ’yan sanda ke niyyar yi a matsayin zancen kanzon kurege kuma masu yada shi suna yin hakan ne don jawo rudani da kuma ba da labaran karya ga al’umma.
Sanarwar ta kara da cewa tun bayana mincewa da Hukumar Kula da Albashi da Daidaito ta kasa ta yi, Ministan Harkokin ’Yan Sanda da kuma Sufeto-Janar ke aiki kafada-da-kafada da Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Tarayya, don tabbatar da an dakatar da harajin da ake yanka daga albashin jami’an ’yan sandan, kamar yadda Shugaban kasa ya bayar da umarni kuma ya samu amincewar Majalisar Zartawa ta kasa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa yana da muhimmanci a sani cewar wannan yunkuri ne na Shugaban kasa, ba tare da neman hakan ba daga hukumar ’yan sanda na neman karin albashi da alawus.
Don haka Gwamnatin Tarayya a shirye take ta kaddamar da sabon tsarin albashin a duk lokacin da aka kammala dukkan shirye-shirye.