A makon jiya ne jagoran Kungiyar Harkar Muslunci a Najeriya ta mabiya Shi’a Sheikh Ibrahim Zakzaky ya fita zuwa kasar Indiya domin a duba lafiyarsa a asibitin Medanta, kamar yadda wata Babbar Kotu ta amince masa. Bayan ya isa kasar shi da matarsa Zeenatu sai ya yi korafin cewa tsaron da ake yi masa a asibitin ko a nan gida bai ga irinsa ba. Hakan ya sa ya zabi ya dawo gida ba tare da an duba lafiyarsa ba, inda ya ce akwai kasashen da suke maraba da shi don duba lafiyarsa. Kan haka wakilanmu sun jiyo ra’ayoyin mutane ko ya dace a ba shi dama ya sake zuwa wata kasa, don a duba lafiyar tasa?
Idan ba zai gudu za a iya sake ba shi dama – Magaji Musa
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Ni ra’ayina shi ne idan an tabbatar Shugaban IMN ta ’yan Shi’a Sheikh Ibrahim Zakzaky ba guduwa zai yi ba, kamar yadda gwamnati take zarginsa akan iya sake ba shi dama, amma idan an tabbatar in aka bar shi ya sake fita wajen don a yi masa magani, akwai wani shiri na zai gudu ne kada a bar shi.
Kamar yadda magoya bayansa suke cewa ba guduwa zai yi a ba shi damar don yana da ’yanci a matsayinsa na xan Najeriya.
Ya kamata a ba shi dama – Yakubu Da’u
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Ina goyon bayan a sake bai wa Sheikh Zakzaky Shugaban IMN ta mabiya Shi’a damar sake komawa jinya a kasar waje. Domin ina ganin hakan zai taimaka a samu lafiyarsa kuma a yi masa shari’a yadda ta dace, don sai da lafiya ake yin komai. Amma abin da ya yi a kasar Indiya alama ce da ke nuni da cewa akwai lauje cikin naxi.
A ba shi dama amma bisa sharaxi – Ado Shu’aibu Xansudu
Daga Abbas Xalibi, Legas
A ra’ayina ya dace a sake ba shi damar sake fita ketare neman lafiya kamar yadda doka ta tsara, amma bisa sharaxin ba shi ne zai zabi asibitin da yake so ba ko kuma likitocin da za su duba shi, domin a yanzu haka a hannun gwamnati yake ita ke da hurumin zabar likitocin da za su kalu da shi, waxanda ta aminta da su. Shawarata gwamnati ta yi abin da ya dace da doka a wannan lamari domin ga dukkan alammu waxansu ’yan adawarta na neman shiga ciki su yi amfani da wannan damar su rika aibantata. Don haka kada ta yi sake a xauki lamarin kamar yadda doka ta tsara wannan shi ne ra’ayina
Ya dace a sake ba shi –Yakubu Ibrahim
Daga Abbas Xalibi, Legas
Eh ya dace a sake bai wa jagoran Kungiyar ’Yan uwa Musulmi ta ’yan Shi’a damar fita waje a duba lafiyarsa domin kuwa koda kana tuhumar mutum da aika ta wasu laifuffuka a hukumance, mutukar yana cikin halin rashin lafiya, to, abu na farko da ya kamata a yi shi ne a ba shi kula ta hanyar yi masa magani. Sannan idan ya warke sai a ci gaba da tuhumar da ake yi masa, wannan shi ne ra’ayina.
Idan dokar kasa ta yarda a bar shi–Mohammed Yusuf Bulama
Daga Muhammad Aminu Ahmad
To na farko dai zan ce dai ba za a yanke shawara ba kai-tsaye ya kamta a duba ta bangaren dokar kasa idan har akwai dokar da ta sake ba shi damar ya sake fita, to ya kamata a bar shi. Saboda a dimokuraxiyya muke idan har akwai dama a kundin tsarin mulkin kasa na a sake ba shi damar a ra’ayina ya kamata a bar shi kawai. Amma a tabbatar da an xauki matakan tsaro kwarara duk inda zai sake fita, kuma idan ya dawo a zartar masa da hukunci daidai da laifin da ake zarginsa.
Ya dace a sake bar shi –Abubakar Lawan
Daga Muhammad Aminu Ahmad
Ni a ra’ayina ya dace a sake barinsa, saboda ya zama kafa hujja ga magoya bayansa, duniya ta tabbata kuma al’ummar kasa su zama shaida, duk da cewa an ba shi dama a karon farko. Kuma gwamnati ta nemi xaya daga cikin kasashen da ya ambata ta tabbatar hulxar jakadacin ta kasance ba sako-sako ba. Domin kada a yi sake ya samu wata kafa ya tsere. Idan an gama yi masa jinya a dawo da shi gaban kotu a ci gaba da shari’arsa.