Da’awa: Akwai da’awar da ke yaduwa a kafafen sadarwar zamani kan amfani da fitaccen maganin cutar maleriyar nan da ake kira ‘P-Aladin’ cewa yana jawo mutane da dama.
Hukunci: Da’awar ba gaskiya ba ce. Bincike ya nuna cewa Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta amince da maganin, kuma babu wani bayani daga manyan kafofin watsa labarai na kasar nan da ya nuna cewa maganin ne yake haddasa mutuwar wadanda suke amfani da shi.
- Shin gwamnati ta saki mayakan Boko Haram kafin ceto fasinjoji jirgin kasa?
- Shin da gaske Ado Gwanja na bata tarbiyyar matasa?
Cikakken Bayani: Sakamakon rasuwar yara 66 a kasar Gambiya saboda jin rauni a koda da ake jingina shi da wasu magungunan tari da aka shigar kasar, sai aka rika yada wani bayani a shafukan sada zumunta ana gargadin ’yan Najeriya cewa kada su yi amfani da maganin zazzabin maleriya na P-Aladin saboda zai iya jawo matsaloli ga koda kuma ya jawo mutuwa.
Sakon ya ce: “Muhimmhiyar sanarwa ta gaggawa. Magani na sama yana nan ko’ina a Najeriya ana amfani da shi a matsayin maganin cutar maleriya.
“Kada wani ya sake saya ko ya yi amfani da shi.
“Yana da guba mai muni da ke cutar da koda.
“Gwaggona ta sha shi don yin maganin maleriya, a karshe maganin ya lalata mata koda.
“Allah Ya ji kanta amin. Don Allah ka isar da wannan bayani ga dangi da abokanka in ka koma gida.”
Mene ne P-Aladin?
A cewar wata kasida da aka buga a kafar PublicHealth.com P- ALADIN, magani ne na ajin Artemisinin (ACTs), magani ne da aka tace shi daga itaciyar da ake kira sweet wormwood.
Ana amfani da maganin idan cutar maleriya ta yi zafi kuma yana taimakawa wajen kashe kwayoyin cutar maleriya kuma yana dauke da wani kaso na sinadaran Dihydroartemisinin 40mg/piperakuine 320mg.
Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ba ta cika son a yi amfani da shi ba, saboda alamun kwayoyin maleriyar suna neman hana maganin aiki.
Shin yana illa ga koda?
Sabanin wannan da’awa, an gudanar da bincike kan yadda rukunin magani na artemisinin zai iya zama maganin cutar koda.
Kan haka Lou Y, a cikin wata mujallar kiwon lafiya ya yi rubutu mai taken, “Nau’o’in magungunan Artemisinin suna iya samar da wata kariya da za ta karfafa magance cutar sankara,” kuma ya kammala da cewa za su iya magance cutar koda tare da bayyanar sababbin hanyoyin kimiyya na ARS.
Wani masanin magunguna, Jelili Kelani, ya shaida wa Aminiya cewa waccan da’awa shifcin gizo ne kawai, “Wani ne kawai ya tayar da kura bisa karya, ba za ka iya gano wanda ya sanya bayanin ba.
“A yanzu babu wani bayani daga Hukumar NAFDAC ko ofishin harhada magunguna da ya ce maganin yana jawo abin da mutumin ya ce.
“Batun shi ne: wane ne wannan mutum? Ba mu san shi ba. Wane mutum ne abin ya shafa? A wane asibitin mutumin ya rasu? Hankali ma ba zai yarda ba.
“Yaya aka yi mutumin ya san cewa koda ce abin ya shafa?
“Eh, kowane magani yana iya kunsar wata guba, hatta Paracetamol.
“P-Aladin rukunin maganin ACT ne mai maganin maleriya.
“Idan P-Aladin yana da matsala to dukkan magungunan ACT suna da shi.
“Sai dai in za a ce nau’in maganin kamfani kaza ne ke da matsalar, amma maganin an tallata shi ya fi a kirga kuma majinyatanmu suna shan sa,” inji shi.
Ya ce, a ce wani magani ne tushen cutar koda, to tun dama mutumin yana dauke da alamun cutar kodar ce, kuma a irin wannan yanayi bai kamata ya sha kowane irin kwayar magani kamar yadda likitoci suke rubuta wa sauran mutane ba.
“Galibi bai kamata ya yi amfani da kwayar magani yadda aka saba ba.
“Idan wannan mutum na da matsala, kamar yana da matsalar koda, idan ya sha kwayar magani yadda saura suke sha, tana iya yi masa illa.
“Don haka ba maganin ba ne ya jawo matsalar,” in ji shi.