✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin karin albashin da aka yi wa ’yan sanda zai magance matsalar cin hanci?

A makon jiya ne aka samu sanarwar cewa Shugaban Kasa ya amince da karin albashi ga ’yanda, wanda hakan ya jefa ’yan sanda da wadansu…

A makon jiya ne aka samu sanarwar cewa Shugaban Kasa ya amince da karin albashi ga ’yanda, wanda hakan ya jefa ’yan sanda da wadansu mutane cikin murna da jin dadi. Wadansu mutane suna murna ne ganin cewa tunda yanzu an samu karin albashi, hakan zai taimaka wajen rage matsalar cin hanci da rashawa. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’yoyin mutane a kan karin albashin, kamar haka:

 

Babu abin da zai rage- Bashir Yusuf

Daga Umar Mikail

Bashir Yusuf: “Ni ina ganin wannan ba abin da zai rage domin matsalar ta riga ta yi girman da har ma ta zama kamar al’ada ce a gare su, domin kuwa yanzu suna ganin cewa idan suka nemi cin hanci ka ki bayarwa kamar hakkinsu ne ka tauye musu. Saboda haka in dai ana so abin ya yi tasiri sosai sai an hada da wani shiri na musamman domin wayar da kan jama’ar gari masu bayarwa da kuma su ’yan sandan.”

 

Karin albashin ba zai magance cin hanci ba – Ibrahim S Bello

Daga Ahmed Mohammed, Bauchi

Ibrahim S. Bello Unguwar Kandahar, Bauchi: “In dai a Najeriya ce, karin albashin da aka yi wa ’yan sanda ba zai magance cin hanci da rashawa ba. Ka ga ko beli da ake cewa kyauta ne, to sai ka biya kudi kuma ba shi zai hana su karbar na goro a hanya ba. To ka ga kuwa sai dai mu ci gaba da addu’a Allah Ya gyara mana Ya kuma ba mu shugabanni nagari.”

 

Karin albashin zai rage cin hanci da kashi 70 daga cikin 100  –Zainab Abubakar

Ahmed Garba Mohammed, Kaduna

Zainab Abubakar:  A ra’ayina karin albashin da aka yi wa ’yan sandan kasar nan zai sa su rage karbar cin hanci da rashawa da kashi 70 cikin 100 saboda tun farko da suna fama da karancin albashi ne shi ya sa mafi yawa daga cikin ’yan sanda suke karbar na-goro.  Don haka yanzu da Gwamnatin Tarayya ta yi musu kari mai gwabi ko shakka babu zai sanya su rage karbar na-goro saboda wani daga cikinsu ba zai so a kore shi daga bakin aiki a kan ya karbi abin da bai taka karya ya karya ba.

Sai dai wani hanzari, duk da wannan karin akwai bukatar a rika biyansu a kan kari, don kada a koma gidan jiya.

 

Karin zai rage matsalar cin hanci– Zainab Mukhtar

Ahmed Garba Mohammed, Kaduna

Zainab Mukhtar:  “Mafi yawancin cin hancn da wadansu daga cikin ’yan sanda ke yi suna faruwa ne saboda karancin albashi sannan da matsalar rashin biyansu a kan lokaci.  Ta yaya za ka sanya wani jami’in tsaro aiki, ka ba shi albashin da bai taka-kara ya karya ba, kuma a mafi yawan lokuta ba a biyansu a kan kari?

Amma a yanzu da ake kokarin yi musu wannan kari, ko shakka babu zai rage matsalar cin hanci da rashawa a cikin ’yan sanda.  Don haka ina kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta kara wa ’yan sanda albashi don a magance wannan matsalar da ta yi katutu.

 

Zai iya rage – Fatihu Muhammad

Daga Umar Mikail

Fatihu Muhammad: “Tabbas zai iya taimakawa amma hakan ba zai magance matsalar gaba daya ba. Dalili kuwa shi ne abin ya dade yana faruwa saboda haka ana bukatar lokaci mai yawa kafin a dakile matsalar gaba dayanta. Da jama’ar gari za su hada kai gaba daya don yakar abin sai ya yi tasiri amma albashi kawai ba zai isa ba gaskiya.”

 

Cin hanci dabia ce– Muhammad Auwal Galadanchi

Daga Ahmed Mohammed, Bauchi

Muhammad Auwal Galadanchi: “In dai mutum mai cin hanci ne ko nawa aka ba shi zai ci, in ba haka ba yaya gwamnoni da manyan ma’aikata ba sa dainawa duk da biliyoyin Naira da suke da su? Karin albashin ba zai hana dan sanda cin hanci ba sai dai in za a sauya tsarin da muke ciki.”