✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin hana almajirci a Kano zai yi tasiri?

Tun sadda Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da sanarwar haramta bara a fadin jihar ake ta cece-ku-ce a kan matakin a tsakanin al’ummar jihar. Yayin…

Tun sadda Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da sanarwar haramta bara a fadin jihar ake ta cece-ku-ce a kan matakin a tsakanin al’ummar jihar.

Yayin da wasu ke goyon bayan tsarin wasu na ganin beken gwamnatin a kan matakin da ta dauka.

Kazalika gwamnatin ta fito da wani shiri na zamanantar da harkar almajirci ta hanyar wajabta shigar da almajirai cikin shirinta na ilimi kyauta kuma dole.

Me dokar hana almajirci ta kunsa?

Dokta Muhammad Sanusi shi ne Kwamisjinan Ilimi na Jihar Kano, ya yi wa Aminiya karin haske game da batun, inda ya bayyana cewa bara kawai aka haramta a jihar, ba karatun allo ba.

“Dokar hana bara dadaddiyar ce a jihar Kano inda aka hana duk wani na’ui na bara ciki kuwa har da wanda almajiran da iyayensu suka kawo su da sunan neman ilimi amma suke bugewa da yawo a tituna suna barace-barace.”

Mene ne sabo a ciki?

“Abin da yake sabo shi ne yadda gwamnatin ke kokarin kawo gyara a harkar almajirci ta yadda aka fito da tsari a harkar koyo da koyarwar gaba daya.

“Gwamnati za ta yi wannan aiki ne bisa madogara da take da ita na dokoki biyu wato Dokar Kananan Yara wadda ta hana sanya yara cikin duk wani aikin wahala da kuma tozartarwa tare da ba su ilimi;

Haka kuma Dokar Ilimin Bai Daya, ita ma ta tanadi wajabcin samun ilimi ga kowane yaro. Wannan ita ce madogararmu.

Mu kuma a nan Kano sai muka ce za mu bayar da ilimin kyauta. Don haka sai muka yi wa shirin take da ‘Ilimi Kyauta kuma Dole’. Wajibi ne kowane yaro ya je makarantar firamaren boko ko kuma wadda za a hada karatun allo da kuma bokon.”

Kwamishinan ya soki lamirin shirin koyarwar na BESDA da Bankin Duniya ya bullo da shi  na koyar da karatun boko a kwanaki biyu a mako.

“Abin ba zai yi ma’ana ba idan aka ce almajiran za su yi karatun boko a kwanakin Alhamis da Juma’a kadai, yayin da sauran takwarorinsu na makarantun boko suke samun karatun sau biyar a mako.”

Sharuddan makarantar allo

Kwamishinan ya jaddada cewa jihar za ta bayar da dama ga wadansu makarantun almajiran su ci gaba da gudanar da harkar bayar da ilimi amma bisa yin aiki da wasu sharudda da gwamnatin ta gindaya.

“Duk wani alaramma da ya shirya bin sharuddan Gwamnati to zai ci gaba da gudanar da Makarantarsa:

“Ya kasance almajiransa suna da wurin kwana ba tare da cunkoso ba. Suna kuma da tsayayyen abinci sau uku a rana.

“Dole sai ya yi wa makarantarsa rajista. Sannan ya amince za a rika koyar da dalibansa ilimin boko da ya hada daTuranci da kuma Lissafi.

“Amma ba zai yiwu ba mutum ya shigo gari ba ya samu wani kango ya ajiye yara sama da dubu, sannan kuma su rika yawo a gari suna barace-barace don neman abinci.”

Shirin samar da isassun makarantu

A cewar Kwamishinan, shirye-shirye sun yi nisa na tabbatar da samar da isassun makarantu da za a ajiye wadannan yara.

Makarantun tsanagaya na gwamnati

A wani jawabinsa, Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ya ce an kammala shirye-shiryen sa almajiran a makarantun kwana wadanda aka riga aka samar wa duk kayayyakin da ake bukata don kulawa da rayuwar yaran.

“Don ganin ta yi amfani da shirinta na samar da ilimi ga almajirai, tuni gwamnati ta samar da makarantun tsangaya na kwana guda uku-uku a kowace Mazabar Majalisar Dattawa uku da ke jihar.

“Za a dauki almajirai a makarantun ciki har da guda 388 da aka dawo da su kwanan nan daga jihohin Gombe da Filato da Kaduna da Nassarawa.”

Baya ga makarantun tsangaya na kwana 12, jihar na duba yiyuwar gyara makarantu 33 na karatun Addinin Musulunci da wasu makarantun fasaha 32 a kananan hukumomi 44 a fadin jihar.

Hukunta iyayen almajirai

A cewarsa gwamnati za ta dauki matakin sharia a kan duk iyayen almajiran da suka ki karbar ‘ya‘yansu wadanda take shirye-shiryen sake damka su a hannun iyayensu.

Abin da ya dace a yi wa almajirai

Shugaban Kungiyar Matasan Alarammomi ta Kasa, Alaramma Muhammad Bayero ya ce ba ya sukar ilimin boko, amma akwai gyara a tsarin gwamnatin na ilmintar da almajirai.

A hirarsa da Aminiya, ya ce akwai bukatar gwamnati ta zauna da alarammomin saboda mai daki shi ya san inda yake masa yoyo.

“Mu muka san kanmu amma ba a zauna da mu ba. Mu ma muna goyon bayan ilimin boko domin a yanzu da girmanmu mun koma makarantar boko har mun san zakin ilimin.

“Ba za mu hana yara masu tasowa su ma su yi ba. Kamata ya yi gwamnati ta fito da tsari mai kyau. Gwamnati ba za ta hana bara ba sai ta samar da abinci ga almajiran.”

Iyayen almajirai

Malam Ibrahim Hassan mazaunin Sumaila mahaifin wani almajiri ne da ke karatu a wata makarantar allo da ke unguwar Kawon Maigari.

Ya shaida wa Aminiya cewa suna goyon bayan karatun bokon da ‘ya‘yansu za su fara matukar ba za a hana su yin na Alkurani ba.

Malam Ibrahim ya ce ba su da karfin daukar nauyin karatun bokon ‘ya‘yansu amma suna fata shirin gwamnati na daukar nauyin yaran zai dore kamar yadda ta yi alkawarin farawa.

Masharhanta

Wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Jihar Kano Malam Haruna Adam na ganin bai dace gwamnati ta ce za ta dauki nauyin almajirai a makarantunsu ba domin ba za ta iya ba.

“Shin a yanzu gwamnatin ta kammala da nata daliban, ballantana ta kara wa kanta wani nauyin da ba za ta iya saukewa ba?

“Kamata ya yi gwamnati ta yi doka cewa idan uba zai kai dansa makaranta, to ya zama wajibi ya dauki nauyin dan nasa.

“Kuma a sanya tsarin koyarwar ya zama irin na wasu kasashe irinsu Bangladesh inda ake koyar da boko da safe da yammaci kuma a koyar da Alkur’ani,” a cewarsa.