Rundunar sojin Isra’ila ta ƙaddamar da abin da ta kira a zaman ‘’taƙaitaccen farmakin ƙasa a ƙaramin waje” zuwa cikin Lebanon ranar 30 ga watan jiya a yunƙurinta na kakkaɓe ƙungiyar Hezbollah daga yankunan Kudancinta.
Farmakin ya ƙara fito da girman yaƙin da Isra’ila ke yi na yaƙar ƙungiyar ta Hezbollah mai gwagwarmaya da makamai da ke samun angizo daga Iran.
Ko makonnin da suka gabata ma, gabanin wannan farmakin, Isra’ila ta yi nasarar lalata hanyoyin sadarwa na Hezbollah ta hanyar tarwatsa dubban na’urorin sadarwa waɗanda ƙungiyar take amfani da su, tare da kashe wasu manyan jami’an ƙungiyar ciki har da shugabanta da ya daɗe yana jan ragamarta wato Hassan Nasrallah, wanda aka kashe a wani hari ta sama. a Beirut ranar Juma’ar ƙarshe a watan Satumba.
Iran ta harba makamai masu linzami a ranar Talata, 1 ga Oktoba inda ta harba makaman masu linzami kusan 200 zuwa cikin Isra’ila, lamarin da ya ƙara zafafa fargabar tankiyar yiwuwar ɓarkewar fito-nafito a a yankin gaba ɗaya.
Yaƙin da Isra’ila take yi a Lebanon ya bayyana yadda ta iya yin gagarumin kutse cikin ƙungiyar ta Hezbollah, inda hakan ya mai do da ƙimar hukumomin leƙen asirin ƙasar, wanda ya dusashe sakamakon gazawar da suka yi wajen hanawa ko bankaɗo harin bazata da Hamas ta kai cikin Isra’ilar a ranar 7 ga Oktoban 2023.
Paul Salem, wani ƙwararre ne a Cibiyar Nazari kan yankin Gabas ta Tsakiya da ke Lebanon ya ce “Wato kacokan Isra’ila ta juya akalar yaƙin a yadda ta zurfafa wajen tattara bayanan asiri game da Hezbollah.
“Wannan wani sabon salon yaƙi ne, kuma hakan ya shammaci Hezbollah da Iran,” in ji shi, yana mai nuni da zurfafa leƙen asirin Isra’ila kan ƙungiyar da kuma hareharen da ta kai wa na’urorin sadarwarta.
“Za a iya cewa Isra’ilar ta yi wa yaƙin 2006 (tsakaninta da Hezbollah), shigar ɗiban karan mahaukaciya – inda tankokin yaƙi ne kawai suka kutsa kan iyakar ƙasar da Lebanon.”
Yakin da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da Hezbollah a halin yanzu ya samo asali ne tun a ranar 8 ga watan Oktoban 2023, lokacin da ƙungiyar masu gwagwarmayan ta Lebanon ta fara harba rokoki zuwa Arewacin Isra’ila domin nuna goyon ƙawarta a gwargwarmay wato Hamas.
Tun daga lokacin ne ɓangarorin biyu wato Isra’ilar da Hezbollah – ke musayar wuta a kusan kullum a kan iyakar Isra’ila da Lebanon.
Sai dai ko a yanzun, masharhanta na cewa yaƙin da take yi da ƙungiyar Hezbollah da kuma bayanan sirrinta, ababuwa ne da aka kwashe shekaru da dama ana shirya su tare da tuna munanan darusan da Isra’ilar yaƙin 2006.
Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙin 2006 cikin gaggawa, ba tare da wani kyakkyawan shiri ba sa’o’i ƙalilan bayan da mayaƙan Hezbollah suka kashe mata sojoji uku tare da yin garkuwa da wasu biyu a wani samame da ƙungiyar ta kai kan iyakar ƙasar.
A lokacin Isra’ilar ta dogara kacokan kan hare-hare ta sama da ta riƙa kai wa kan kafofin Hezbollah, amma a rana ta huɗu da soma kafsawar, sojojin Isra’ilar ta fara kai hare-hare kan jerin muhimman wurare 83 da jami’an leƙen asirinta suka tattara kafin yaƙin.
Rikicin, wanda ya sanya Isra’ilar tura sojojin ƙasa zuwa Kudancin Lebanon, a ƙarshe dai sai da aka kwashe kwanaki 34 ana gwabzawa, inda aka kasa cimma matsaya har sai da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kafa Ƙudurin Kwamitin Sulhun majalisar mai lamba 1701, da nufin kawo ƙarshen faɗan.
A wancan lokacin dai fiye da ‘yan ƙasar Lebanon 1,000 ne aka kashe a yaƙin, inda ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta riƙa kai wa a matsayin musabbabin mutuwar fararen hulan.
An yi ta yi wa yaƙin kallon wani abin kunya ga gwamnatin Isra’ila wanda hakan ya sa mahukuntan ƙasar ɗaukar tsawon lokaci suna nazartar yaƙin a tsakanin jami’an soji da na leƙen asirin ƙasar.
Matiyu Levitt, masani kan yaƙi da ta’addanci da leƙen asiri a Cibiyar Washington kuma mawallafin littafin Hezbollah: The Global Footprint of Lebanon’s Party of God ya ce: “Sun yi (Isra’ilar) matuƙar karatun ta-natsu kan yadda suka gudanar da yaƙin na 2006. Ina ganin a fili yake cewa a lokacin ba su da isassun bayanai game da ƙarfin Hezbollah.”
Sojojin Isra’ila sun kuma sake yin nazarin ko tunanin yadda yaƙin da zai sake ɓarkewa tsakaninsu da Lebanon zai iya kasancewa, in ji Leɓitt.
Manyan jami’an Hezbollah 7 da Isra’ilar ta kashe cikin mako ɗaya
A cikin mako guda, wato tsakanin 20 zuwa 29 ga watan jiya – hareharen da ƙasar Isra’ila ta kai a Lebanon, sun hallaka wasu manyan kwamandoji bakwai da jami’an ƙungiyar gwagwarmaya ta Hezbollah, ciki har da shugaban ƙungiyar Hassan Nasrallah.
Matakin dai ya jefa ƙasar Labanon da ma yankin Gabas ta tsakiya cikin kaɗuwa yayin da jami’an Isra’ilar suka yi ta murnar manyan nasarorin soji da na leƙen asirin da suka samu.
Ƙungiyar Hezbollah dai ta sanya wasu dakaru domin fafatawa a matsain wani ɓangare na goyon bayan ƙawarta Hamas a Zirin Gaza kwana guda bayan harin ba-zata da ƙungiyar Falasɗinawan ta kai a Kudancin Isra’ila.
Hare-harenbaya-bayan nan Isra’ilar take kai wa Lebanon da kuma kisan Nasrallah sun zama manuniyar ƙazancewar yaƙin da ake kwabasawa a yankin Gabas ta Tsakiya, a wannan karon tsakanin Isra’ila da Hezbollah.
Rundunar soji da siyasa mafi ƙarfi a Lebanon a yanzu – Hezbollah – ta sami kanta a mummunan yanayin neman yadda za ta murmure daga mahangurɓar da aka yi mata, inda ta yi hasarar manyan mambobinta mafi muni cikin shekaru tun bayan kafuwarta a farkon shekarun 1980.
Babban cikinsu shi ne Hassan Nasrallah, wanda aka kashe a wasu jerin hareharen da Isra’ilar ta kai ta sama da suka lalata gine-gine da dama a Kudancin Beirut. Har ma da wasu jiga-jiganta da ba su yi shuhura a idon duniya ba, duk da cewa suna da matuƙar tasiri a aikaceaikacen ƙungiyar Hezbollah.
1 – Hassan Nasrallah 2 -Nabil Kaouk 3 -Ibrahim Akil 4 -Ahmad Wehbe 5 -Ali Karaki 6 -Muhammad Surajo 7 -Ibrahim Kobeis
Sannan an kashe wasu manyan kwamandojin a yayin farmaki daban daban.
Cikin yardar mai duka, a mako mai zuwa za mu kawo bayanan manyan kwamandoji da jami’an ƙungiyar da Isra’ilar ta yi nasarar hallaka wa ciki har da Ibrahim Aƙil da hukumar leƙen asirin Amurka CIA ta shafe shekaru 41 tana farautarsa.