Fitowar Sanata Aishatu Dahiru Ahmed a baya-bayan nan ta haifar da ce-ce-ku-ce kan ko ’yar takarar Gwamna a Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa a 2023 na shirin sake tsayawa takarar gwamna domin cika burinta na zama gwamna mace ta farko a kasar na?
Tun bayan da Kotun Koli ta yanke hukunci a kan zaben Gwamnan Jihar Adamawa a 2023 a watan Janairu, Sanata Aishatu ta ci gaba da zama a bayan fage har sai da ta bayyana a jama’a a farkon wannan watan.
- Sana’ar Bola-jari: Muna taka sawun barawo — Shugaban ‘yan gwangwan
- ’Yan sanda sun ƙwace sakamakon zaɓe a Ribas
Sake bayyanar ta haifar da tattaunawa a tsakanin masu lura da harkokin siyasa da magoya bayanta.
Wadda aka fi sani da Aisha Binani, Sanata Ahmed na gab da kafa tarihi a matsayin mace ta farko da ta taba zama gwamna a Nijeriya kafin Kotun Koli ta dakile burinta.
Kotun Kolin ta yanke hukuncin cewa, Shugaban Hukumar Zaben da ya bayyana ta a matsayin wadda ta yi nasara, yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zabe, ba shi da hurumin yin hakan.
Binani ta nemi Kotun Kolin kasar da ta tabbatar da sanarwar da Hudu Yunusa-Ari, wanda aka dakatar da shi, ya yi, inda ya bayar da misali da sashe na 149 na Dokar Zabe.
Ta ce, Yunusa-Ari, a matsayinsa na wakilin Hukumar Zabe kasa (INEC), ya yi aiki da ikon da doka ta ba shi.
Sai dai kotun ta ki amincewa da hakan, inda ta kara da cewa dole ne a bi ka’idojin zabe kuma ba za a sanar da sakamakon zaben ba har sai an kammala tattara sakamakon.
Sarkakiyar zaben 2023 a Adamawa ya yi nuni a kan kan ayyukan cikin gida na Hukumar INEC, wanda ya haifar da ayar tambaya game da yadda za a gudanar da zabe da kuma rawar da Hukumar Zabe ke takawa wajen tabbatar da gaskiya da adalci.
A wajen Binani wannan babban koma-baya ne a yunkirinta na kafa tarihi a siyasar Nijeriya.
Dawowa cikin al’umma
Bayan watanni da yin nusau a cikin al’umma, dawowar Binani fagen siyasa ya sake nuna irin sha’awar da take da ita a siyasa.
Ayyukanta na baya-bayan nan, musamman na nuna godiya da nufin sake haduwa da magoya bayanta, ya sa mutane da yawa na ganin cewa ta fara zawarcin sake tsayawa takarar kujerar gwamna.
A wani taro da ta yi a Yola, babban birnin jihar, Binani ta nuna jin dadinta ga magoya bayanta, wadanda yawancinsu daliget ne zaben-fid-da gwani na gwamna a Jam’iyyar APC.
A wajen taron, wanda daruruwan daliget, Binani ta raba buhunhunan taki guda 1,000, inda kowanne daga cikin daliget 430 ya samu buhu mai nauyin kilo 50.
Ana kallon abin da ta yi a matsayin nuna sadaukarwa na ci gaba da jajircewarta a fagen siyasarta da kuma nuni da cewa tana da niyyar ci gaba da yin tasiri a fagen siyasar Adamawa.
Daya daga cikin makusantanta, Julius Kadara, tsohon kwamishina, ya yaba mata bisa nuna godiya ga wadanda suka tsaya mata, inda ya bayyana abin da ta yi a matsayin wani abu da ba kasafai ake yin saba a fagen siyasar Nijeriya, inda yawancin ’yan siyasa ke ci gaba da rayiwarsu ba tare da nuna godiya ga magoya bayansu ba bayan wucewar kakar zabe.
Bayan wannan taron, Binani ta ziyarci Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, inda ta bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 don tallafa wa wadanda iftila’in ambaliyar ruwa afkawa a Maiduguri da Jere a kwanakin baya.
Wannan karamci ya kara fito da ita a siyar kasar nan, inda kara jaddada sadaukarwarta ga ayyukan ji-kai.
Sabon yunkurin kaiwa ga Gidan Gwamnatin Adamawa?
Aikace-aikacen Binani na bayabayan nan ya sa masu nazarin harkokin siyasa hasashen cewa ayyukan nata wani bangare ne na dabarun sake tabbatar da burinta na takarar gwamna a zaben 2027.
Duk da yake ba ta yi wata sanarwa a hukumance ba, ayyukanta sun nuna cewa tana shirin sake shiga daga domin a faffata da ita.
Idan aka yi la’akari da kwazon da ta yi a zaben 2023, mutane da yawa sun yi imanin cewa ta yi kokari sosai.
A zaben gwamna na 2023, Binani ta samu kuri’u 398,788, yayin da gwamna mai ci Ahmadu Fintiri ya samu kuri’u 430,861, kamar yadda sakamakon karshe na INEC ya nuna.
An bayyana yadda ta tara kuri’u masu yawa irin wannan, duk da kalubalen da ta fuskanta.
Salon siyasa na musamman
An yaba wa Binani bisa yadda ta yi hulda kai-tsaye da masu zabe, wanda ya bambanta ta da sauran ’yan siyasa a Nijeriya, wadanda galibi ke dogaro da masu shiga tsakani wajen kaiwa ga masu zabe.
Wannan salon ya sanya ta a zukatan jama’ar Adamawa da dama, da hakan ya sa ta zama ‘yar siyasar da sunanta zai yi ta amo a shekaru masu zuwa.
Manazarta dai na ganin yiwuwar samun nasarar Binani a shekarar 2027 na iya kara tagomashi ne lura da cewa Gwamna Fintiri ba zai sake tsayawa takara ba, domin da ya kammala wa’adinsa na biyu zuwa lokacin.
Gwamnan da kansa ya riga ya yi nuni da muhimmancin wanda zai gaje shi ya zama dan siyasa na ainihi kuma na gari, wanda zai sanya jin dadin jama’a gaba da komai sannan ya zama mai sadaukarwa domin ci gaban jihar – halayen da an kusa yin ittifakin cewa tana da su.
Rikicin siyasar Binani ya riga ya ga cewa ta cimma nasarori da dama.
A shekarar 2022 ta samu tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC bayan ta fafata da maza 5 da suka hada da tsohon gwamna Jibrilla Bindow da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu.
Manazarta dai na ganin yiwuwar samun nasarar Binani a shekarar 2027 na iya kara karfi ganin cewa Gwamna Fintiri ba zai sake tsayawa takara ba, domin da ya kammala wa’adinsa na biyu zuwa lokacin.
Gwamnan da kansa ya riga ya yi nuni da mahimmancin wanda zai gaje shi ya zama dan siyasa na gari, wanda ke ba da fifiko ga jin dadin jama’a kuma yana son sadaukarwa don ci gaban jihar wadanda Binani take da su.
A shekarar 2019, ta zama ‘yar majalisar dattijai mace daya tilo daga arewacin Najeriya a majalisar wakilai ta tara, inda ta nuna gagarumar nasara a yankin da mata ke fuskantar cikas wajen shiga harkokin siyasa.
Kafin zamanta a majalisar dattawa, ta taba zama ’yar Majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar Yola ta arewa/Yola ta kudu/Girei daga 2011 zuwa 2015.
Duk da haka, tafiyar siyasarta ba ta kasance ba tare da ƙalubalen ba, musamman a ƙoƙarinta na zama mace ta farko ta gwamna a Adamawa.
Bayan cikas da al’adun siyasar Najeriya maza ke haifarwa, Binani ta fuskanci ƙarin nauyi na rashin son rai na al’umma da na al’ada wanda galibi yakan shafi mata masu neman mukamin siyasa.
Yunkurin da ta yi na bin sahun marigayiya Aisha Alhassan—wanda aka fi sani da “Mama Taraba” ya bayyana a matsayin abin lura.
Mama Taraba, wacce ta rasu a shekarar 2021 tana da shekaru 61, ta kusan zama zabbiyar gwamna mace ta farko a Nijeriya a shekarar 2015, lokacin da wata kotu ta soke sakamakon zaben da aka yi mata.
Sai dai kotun daukaka kara da Kotun Koli sun soke hukuncin, lamarin da sa Binani ta yi ta bin wasu hanyoyi.
A wata hira da aka yi da ita a baya, Binani ta bayyana hangen nesanta da dabarun karfafa mata da matasa, inda ta ce: “A lokacin yakin neman zabena, na shaida wa matan cewa, zabena zai amfani ’ya’yansu.
“Idan suna da diya mace, za su yi mata alheri ta hanyar zabena; za su samu wannan tagomashi ga ’yar’uwa, kuma har zuwa wani lokaci, ga mahaifiyarsu.
“Na yi alkawarin cewa zan ba da fifiko ga al’amuran mata da matasa, musamman ma ’ya mace.”
Wannan roko na jin dadin jama’a ya yi tasiri ga dimbin al’ummar da suka zabe su, musamman mata, wadanda ke ganin takararta a matsayin wata dama ta sauya fasalin kasa.
Masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin sakon nata bai wuce kalaman siyasa kawai ba, yayin da ta yi magana kan sauyin al’adu da wasu ke ganin ana bukata a siyasar Nijeriya domin samun wakilci da karfafawa mata da matasa.
Binciken masana a kan makomar siyasar Binani
Dr. Kabiru Sufi, fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa ne da ya bayyana wa Weekend Trust ra’ayin cewa, akwai yuwuwar Binani ta sake tsayawa a 2027.
Bayan da ta yi nusau na wasu watanni, da alama za ta kimanta zaben 2023 da nufin sake dabaru, Dr. Sufi ya yi imanin cewa, yana da matukar muhimmanci ta dawo fagen siyasar da wuri.
“Abin da ta yi a zaben 2023 abu ne mai ban mamaki, kuma watakila za a iya cewa ba a taba yi ba, duba da irin kuri’un da ta samu da kuma yadda ta fito a matsayin ’yar takarar APC.
Taimakon da ta samu daga mata da matasa, ba kawai a Adamawa ba har ma a fadin kasa, ya yi tasiri, kuma ba za ta bari hakan ya dushashe ba.
“Amma dole ne ta gane cewa, samun tikitin takara a 2027 zai zo da gagarumin kalubale, kamar yadda ya faru a 2023.
“Za ta kuma so ta tabbatar da cewa wasu jiga-jigan ’yan siyasa daga jiharta da ke rike da mukaman a tarayya b asu disashe hasken ta ba.
“Abin da ke da tabbas shi ne idan ta sake fitowa takarar, za ta bai wa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar wahala.
“Babu shakka kasancewarta zai sa zaben ya fi daukar hankali a ciki da wajen Jihar Adamawa.
“Tushen tallafin da take ba da umarni yana da mahimmanci,” in ji shi.
Ana sa ran zuwa 2027
Tare da goyon bayan kafaffen hanyar sadarwar siyasa da ta haɓaka sama da shekaru ashirin, burin Binani na neman takara karo na biyu a kujerar gwamna yana da ƙarfi.
Masu sharhi kan harkokin siyasa irin su Dr. Sufi sun yi nuni da cewa, gogewar da ta samu, hade da kimarta a matsayin ’yar takarar da ke jan hankalin mata da matasa, na iya zama mabudin nasarar da za ta samu a 2027 idan har ta sake yanke shawarar tsayawa takara.