✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin Babban Alkalin Najeriya ya kamu da COVID-19?

Ofishin Mai Shari’a Tanko Muhammad ya ce yana birnin Dubai ana jinyarsa saboda rashin lafiya

Babban Alkalin Najeriya (CJN), Mai Shari’a Tanko Muhammad (SAN) ya harbu da cutar COVID-19, a cewar rahotanni.

Jaridari harkokin shari’a ta intanet, Nigeria lawyer, ta ce wani Alkalin Kotun Kolin Najeriya ne ya sanar kamuwar Mai Shari’a Tanko Muhammad da COVID-19 a Hedikwatar Kungiyar Lauyoyi Musulmai ta Najeriya (MULAN) da ke Abuja a ranar Talata.

Alkalin na Kotun Koli ya ce an gano Mai Shari’a Tanko na dauke da COVID-19 ne bayan gwajin cutar da aka yi masa a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ake jinyar sa.

Kakakin Babban Alkalin na Najeriya, Festus Akande, ya tabbatar da cewa Mai Shari’a Tanko Muhammad na Dubai ana jinyarsa, sai dai bai bayyana rashin lafiyar da ke damun mai gidan nasa ba.

 

Kotun Koli ta musanta labarin

Sai dai Kotun Koli ta Najeriya ta bakin Daraktan Yada Labaranta, Festus Akande, ta ce babu wata takardar asibiti da ke nuna CJN Tanko Muhammad ya harbu da COVID-19.

“Masu yada labarin su kara bincikawa daga majiyar tasu su kuma samo sakamakon gwajin da ke tabbatar da karyar tasu.

“Zuwa yanzu, babu wanda ya kawo min ko ya kawo wa wani a Kotun Koli sakamakon gwajin da suke ambata a rahoton”, inji Akande.

Sanarwar da ya fitar ta kara da cewa babu kanshin gaskiya a labarin da ake yadawa game da lafiyar Mai Shari’a Tanko Muhammad.

“Daya karyar ita ce ikirarin cewa CJN din ya shafe makonni ba tare an gan shi ba a bainar jama’a.

“Muna mamakin inda dan jaradar ya samu wannan bayani, domin CJN ya yi ta gudanar da harkokinsa, har ya rantsar da sabbin Alkalan Kotun Koli a makonnin baya”.

 

Babban Alkalin Najeriya bai halarci rantsar da sabbin Manyan Lauyoyi ba

A ranar Litinin mun kawo rahoto cewa Babban Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Tanko Muhammad bai halarci taron rantsar da sabbin Manyan Lauyoyin Najeriya (SAN) 72 ba.

Bisa al’ada, mai rike da ofishinsa ne ke jagorantar taron na shekara-shekara a Kotun Kolin Najeriya wanda ke gudana ranar Sabuwar Shekara ta Kotun Kolin.

Babbar Alkalin Kotun Koli, mai biye da shi, Mai Shari’a Olabode Rhodes-Vivour ce ta wakilce shi wurin jagorantar taron da kuma rantsar da sabbin SAN-SAN din.

A lokacin taron na 2020, ba a bayyana dalilin rashin halartar Babban Alkalin Najeriyan ba.

Alkaluman da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce zuwa ranar Litinin 14 ga Disamba, 2020, mutum  73,371 ne suka kamu da cutar ta COVID-19 a Najeriya.

A watan Fabrairun 2020 ne cutar da ta samo asali daga birnin Wuhan na kasar China ta fara bulla a Najeriya.

A jihohin Legas da Abuja ne cutar ta fi kamari, har ta kai ga an sanya dokar hana fita a fadin Najeriya lokacin cutar da take ganiyarta.

 

COVID-19 ta sake dawowa

A halin yanzu, makonni kadan bayan janye dokar hana fita, mahukunta na bayyana fargaba kan sake bazuwar cutar a karo na biyu, tare da alamta yiwuwar dawo da dokar hana fitar.

Kwamitin Yaki da cutar da Shugaban Kasa ya kafa sun yi zargin dawowar yawaitar masu cutar a kan yadda kungiyoyin addinai ke ci gaba da gudanar da manyan taruka da ke iya sama hanyar yaduwar cutar.

Ya kuma bayyana damuwa bisa yadda jama’ar kasa suka yi watsi da bin matakan kariyar cutar.

Zuwa yanzu dai Gwamnatin Jihar Kaduna ta rufe makarantu a fadin jihar, sakamakon hauhawar sabbin masu cutar.

Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai  ya killace kansa bayan sakamakon gwaji ya nuwa wasu makusantansa sun kamu da cutar a ranar Asabar.

Jihar Kano ma ta bayyana damuwa kan yadda ake samun karuwar masu kamuwa da cutar.

Gwamnatin Jihar ta umarci ma’aikatan sa-kai kan yaki da cutar ta da sau dawo bakin aiki a yunkurinta na gamawa da cutar.