Abubuwan da ake gani yanzu a ma’aikatu da makarantu da kasuwanni da tituna da sauransu sun isa tabbatar da cewa tsiraici ya gama cinye matan Musulmi. Matan sukan sanya tufafi matsattse ko dangalalle ko shara-shara ko kuma mai daukar hankali, har ma aka kirkiro da salon dinkuna tare da sanya musu suna, misalansu: ‘Jahannama-ga-fasinja’ da ‘Zage-zub-mu-shana’ da ‘Zuro-hannunka-masoyi’ da ‘Baba-ga-kiwonka’ da ‘Masoyi-me-ka-gano? da ‘Kalle-ni-ba-ciko-ba-ne’ da ‘A-tsokani-shari’a’ da ‘Filashin’ da kuma ‘kwalelenku-samari’, bugu da kari ga na Turanci irin su ‘show me back’ da ‘cospy tops’ da ‘pallazo pants’ da ‘bell bottom’ da ‘spaghetti’ da sauransu.
Matan da ke sanya irin wadannan tufafin babu abin da ya sha musu kai, gani suke duk wacce ba ta yi, to ba ta waye ba, duk da cewar Manzo SAW ya ce: “Zai kasance a cikin karshen al’ummata wasu mata sun sa tufafi amma tsirara suke, a bisa kawunansu kamar tozon rakumi, ku tsine musu domin su tsinannu ne.” Kada a manta duk tausayin da Manzon Allah SAW yake da shi amma ya ce a tsine wa wasu daga cikin al’ummarsa, haka ya tabbatar da sun dauko da zafi.
Hijabi umarnin Allah ne inda yake cewa: “Ya kai Annabi ka ce wa matanka da ‘ya’yanka da matan muminai su kusantar da kasa daga manyan tufafin da ke kansu…”Ahzab 59. Ke nan masu shigar tsiraici suna ganin umarnin Allah kauyanci ne? Wa iyazu billah! Suna yin izgili ga masu sanya hijabi.
Hijabi tufafi ne mai kauri, marar ado kuma dogo har kasa, duk wanda ba haka yake ba to ba sunansa hijabi ba.
Manzon Allah SAW ya ce: “Dukkanin al’ummata ana yafe musu laifuffukansu, amma ban da masu bayyanar da sabo.” (Minhajil Mu’umin shafi na 231). Yanzu matse kugu da fitar da nono ba bayyanar da sabo ba ne? Kuma masu hakan na ganin babu wanda ya isa ya hana su, shi ya sanya ba su jin kunyar a gan su, suna yi ne don a ce sun waye (ta banza), sun manta yadda Musulunci ya suturta su amma suka tsiraice!
Sannan matsalar wasu masu bakar zuciya daga cikin mutane ita ce, suna cewa ai duk masu sa dogon hijabin su ne ‘yan iskan, ga tambaya, to ku da ba ku sawa su wane ne? Idan ma wani ya ce haka ai ba duka aka taru aka zama daya ba.
Ga iyaye
Amma abin mamaki iyayen masu shigar tsiraicin nan suna gani sun kyale; wasu iyayen ma su ke sa a dinka wa ‘ya’yansu tufafi masu bayyanar da tsiraici. Manzon Allah (SAW) ya ce “Dukkanku masu kiwo ne, kuma sai an tambaye ku a kan kiwon da aka ba ku…” Bukhari da Muslim. Allah SWT Ya ce: “Ya ku wadanda kuka yi imani, ku kare kanku da na iyalanku daga wata wuta makamashinta mutane da duwatsu ne. A kan ta wadansu Mala’iku ne masu kauri da karfi, ba su saba wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma suna aikata abin da ake umurninsu.” Tahrim, aya ta 6.
Amma iyaye sun kyale ‘ya’yansu na yawo tsirara har ma wasu ka ji suna cewa: “A kyale su zamani ne.” Domin Manzon Allah SAW ya tabbatar da duk wacce take bayyanar da tsiraici ’yar wuta ce. Ya ce: “Nau’in mutane guda biyu na daga cikin ‘yan wuta har yanzu ban gan su ba, wasu mutane tare da su akwai bulali kamar bindin shanu suna bugun mutane da su, da wasu mata sun sanya tufafi amma tsirara suke….. wadannan mata ba za su shiga aljanna ba…” Duba Al-Kaba’ir shafi na 139.
Mazaje
Haka za ka ga wadansu mazaje sun bar matansu suna shigar tsiraici, irin wadannan mazaje ake kira Duyith, wato Allah Ya tsine musu.
Ga teloli
Teloli suna ba da gudunmuwa mai tsoka a bangaren shigar tsiraici. Duk wani irin salon da aka gani na shegantaka su ne suke fito da shi, kasancewar su ne suka dinka shi. Idan suna ikrarin ai cewa aka yi su dinka, sun manta Allah SWT Ya ce a taimaki juna da aikin kwarai, a kuma guji yada barna? Don haka ya kamata teloli su ji tsoron Allah.
Wasu daga cikin matsalolin shigar banza:
1 Babu mutumin kirkin da zai auri mai bayyanar da tsiraicinta. 2 ‘Yan iska na iya yi mata fyade saboda tayar musu da sha’awa ko kuma ya kai zuwa ga zina. 3 Kowane sakarai zai iya kokarin tsayar da ita a titi saboda ya ga irin tasu ce. 4 Ana mata kallon ‘yar iska marar tarbiyya a muhallin da take. 5 bata tarbiyyar al’umma domin mai yi tana koya wa kanana masu tasowa.
Allah Ya taimake mu, amin.
Kabir Sa’idu Dandagoro (Bahaushe), shi ne wakilin Mujallar Muryar Arewa, a Katsina.
Za a iya samunsa a wannan lambar: 08038387516 ko Kibdau:[email protected]
Shigar tsiraici: Wayewa ko tabewa?
Abubuwan da ake gani yanzu a ma’aikatu da makarantu da kasuwanni da tituna da sauransu sun isa tabbatar da cewa tsiraici ya gama cinye matan…