Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya gana da gwamnonin jihohi 36 game da sabon albashi mafi ƙarancin albashin ma’aikatan ƙasar da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki.
Shettima da gwamnonin har da ministoci sun gana a taron majalisar tattalin arziki ta kasa karo na 141 da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
- Majalisa ta amince a tsawaita wa’adin aiwatar da Kasafin Kuɗin 2023
- Nijeriya ta karɓi bashin N7trn a rubu’in farko na 2024 — DMO
Mataimakin shugaban ƙasar ne ya jagoranci tattaunawar da gwamnoni da mataimakansu da kuma ministoci kafin isowar Shugaban Kasa Bola Tinubu.
Taron ya zo ne kwanaki biyu bayan da majalisar zartaswar gwamnatin tarayya ta jinginar da batun mafi kankantar albashin domin ba da dama a kara yin tuntuba.
Daga cikin gwamnonin da suka hakarci zaman sun haɗa da Usman Ododo (Kogi), Uba Sani (Kaduna), Lawal Dauda (Zamfara), Charles Soludo (Anambra), Seyi Makinde, (Oyo), Lucky Ayedatiwa, (Ondo).
Sauran sun haɗa da; Abdullahi Sule, (Nasarawa), AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara), Caleb Mutfwang, (Filato), Hope Uzodimma (Imo), Biodun Oyebanji, (Ekiti), Muhammed Inuwa Yahaya, (Gombe), Peter Mbah, (Enugu), Francis Nwifuru (Ebonyi), Dapo Abiodun, (Ogun), Umar Radda, (Katsina), Abba Yusuf (Kano), Umar Namadi, (Jigawa) da Umar Bago (Neja).
A ranar Laraba ne gwamnoni ƙarƙashin ƙungiyar gwamnonin Najeriya suka gana a Abuja inda suka bai wa ’yan kasar tabbacin cewa tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kansu da kuma kungiyar kwadago zai yi tasiri.
Shugaba Bola Tinubu a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya ya bai wa ƙungiyar kwadago tabbaci cewa nan ba da dadewa ba za a aike da kudiri kan sabon albashi mafi kankanta zuwa ga majalisar dokokin kasar domin amincewa.
Ana sa ran shugaban zai ɗauki mataki kan shawarar N62,000 da gwamnati ta bayar da kuma buƙatar ’yan kwadago ta neman mafi kankantar albashi a Najeriya ya zama N250,000.