Gwamnan Jihar Katsina Barista Ibrahim Shema ya kaddamar da sabon fasfo na zamani a hukumar shigi da fici ta jihar ta a ranar Alhamis din makon jiya inda ya yaba wa hukumar kan yadda take inganta ayyukanta.
Gwamnan ya kuma nuna damuwarsa a kan rashin daukar fasfo da muhimmanci inda ya ce, a wasu kasashen nemansa ake yi amma ba su samu, inda ya kawo misali da irin yadda mutanan Nezalan suke mamaki a kan rashin kular ’yan Najeriya wajen mallakar fasfo.Ya yi kira ga matafiya su yi kokarin mallakarsa, inda ya kawo misali da wanda ake yi a tsakanin kasashen Afirka ta Yamma da ya ce za su zamo kariya ga matafiyi. Kwantarolan hukumar Mista Emmual N. Ogbomou ya ce, sabon fasfon zai magance wasu matsalolin da aka fuskanta a baya, musamman amfani da sama da mutum daya a wasu wurare. Kwantarolan ya ce, kasancewar an tsara shi ta hanyar adana wasu bayanan sirrin a intanet zai yi wuya a musaya hoton wani ko sunansa ko kasar da ya fito ba tare da an gane ba. Kwantarolan ya ja hankalin al’ummar Jihar Katsina musamman matafiya kan su yi kokarin mallakar fasfo din ko saboda dalilai na tsaro.
Shema ya koka kan rashin karbar fasfo daga jama’a
Gwamnan Jihar Katsina Barista Ibrahim Shema ya kaddamar da sabon fasfo na zamani a hukumar shigi da fici ta jihar ta a ranar Alhamis din…