✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shaguben Shekarau ga Ganduje: Wane ne jagoran cushe-cushe?

Shekarau ya yi shagube bayan Ganduje ya zarge su da rashin aiki da kudaden da suke samowa daga Abuja.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya yi wa gwamnan jihar mai ci Abdullahi Ganduje, raddi inda ya yi mishi shagube da cewa jagoran cushe-cushe.

Shekarau ya yi shaguben ne a wani taron siyasa a gidansa da ke titin Mundubawa a Kano, kwana biyu bayan wani taron siyasa ga Gwamna Ganduje ya gudanar a Gidan Gwamnatin jihar Kano.

A jawabin Shekarau ga taron da ya gudana a ranar Talata ne ya yi gugar zana da cewa, “Alhajiji ya ce shi ne shugaban karbe-karbe. Amma ina jiran sa ya gaya wa ’yan Kano waye shugaban cushe-cushe?”

Malam Ibrahim Shekarau na fadar hakan, magoya bayansa da ke halartar taron suka yi ta sowa suna hayaniya a wurin taron.

Ana ganin shaguben na tsohon gwamnan raddi ne ga kalaman Ganduje wanda ya zargi Sanata Shekarau da Sanata Barau Jibrin suna karbar kudade a matsayin ’yan Majalisar Dattijar ba tare da yi wa jama’ar mazabarsa komai ba.

A wurin taron, Ganduje ya ce Sanata Barau da Malam Shekarau, wadanda ke zaman doya da manja da shi, sun “Kasa yi wa jama’ar mazabarku muhimman ayyukan raya kasa, to me zai so ku dora wa mutane laifi idan kuka fara samun matsala?

“Jama’ar mazabarku ba su san inda kudaden da kuke karbowa daga Abuja suke shigewa ba, to laifina na me za ku gani? Me ya sa za ku dora min laifi kan matsalolinku?,” inji Ganduje, cikin gugar zana.

An dai jima ana dambarwa a Jihar Kano game da wani bidiyo da ke nuna wani mutum yana karbar kudade yana cusawa a aljihu, wanda ake zargin cewa gwamnan ne a lokacin da yake karbar toshiyar baki daga hannun wani dan kwangila a jihar.

– Rikicin siyasar siyasar Kano

Rikicin siyasa a jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ya kara dagulewa ne a baya-bayan nan inda Shekarau da Sanata Barau Jibrin da wasu ’yan Majalisar Wakilai daga jihar, ciki har da Honorabul Sha’aban Ibrahim Sharada, suka kafa tsaginsu.

Lamarin ya kai har bangaren na Shekarau ya kai wa Kwamitin Rikon Uwar Jam’iyyar APC karar Ganduje da neman birkita al’amuran jam’iyyar a Jihar.

Ko a zaben shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar da Jihar Kano, bangaren Shekarau ya gudanar da nashi na daban, inda ya zabi Alhaji Haruna Zago a matsayin Shugaban Jam’iyyar, reshen Jihar Kano.

A lokacin da yake jawabi ga taron na ranar Talata, Malam Ibrahim Shekarau ya ce koka game da abubuwan da ke faruwa a jam’iyar da har suka kai shi ga yakicewa ya kafa bangarensa.

A cewarsa, ya yi hakan ne domin ya kwatar wa ’yan jam’iya da al’ummar Kano ’yancinsu.

Ya yi zargin cewa tun da Ganduje ya yi gayyar ’yan jam’iya suka roke shi ya shiga APC, a ka ci zabe, gwamnan ya yi watsi da shi.

Ya ce hatta zaben shugabannin jam’iya na mazaba da kananan hukumomi da na jiha, gwamnan ne ya ci karensa babu babaka ba tare da an tafi da mutanensa ba.

%d bloggers like this: