A ranar Juma’a wata kungiyar Musulmi daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya za ta kaddamar da Alkur’anin da ta fassara zuwa harshen Ibo.
Daya daga cikin mambobin kungiyar ta Ibo Muslims D’awah Group, Malam Muhammad Muritala Chukuemeka ne ya bayyana hakan a ziyarar girmamawa da kungiyar ta kai Hedikwatar kamfanin Media Trust masu wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya da dangoginsu da ke Abuja ranar Talata.
- Babu gudu ba ja da baya kan daukar bindiga don kare kai —Matawalle
- Masu gadi sun saci ‘Corn Flakes’ ta Naira miliyan 2 a Legas
“Yanzu haka muna da kwafi 500 na wannan fassarar Alkur’ani, kuma mun aika guda 100 zuwa yankin Kudu maso Gabas domin ci gaba da aikin da’awa ga ’yan uwanmu ’yan kabilar Ibo, don haka ina kira ga sauran al’ummar Musulmi da su yi koyi da hakan domin kara yada addinin Allah”, in ji shi.
Ya bayyana cewa shi da sauran ’yan uwansa da ke kungiyar sun yi silar musuluntar al’ummar Ibo da dama ba ya ga aikin tarjamar Al’kuranin da suka shafe shekara biyar suna yi.
Malamin wanda haifaffen garin Orlu ne da ke Jihar Imo, ya yi kira ga al’umma da su daure su halarci bikin kaddamar da A’lkuranin da za a yi bayan Sallar Juma’a a Masallacin Ansaruddeen da ke Unguwar Maitama a Abuja.
Ya kuma yi kira ga Musulmin Najeriya da su zauna lafiya da juna, domin kuwa Musulinci addinin zaman lafiya ne da ya haramta kisan ba gaira ba dalili.