Shekara guda da hawansa mulki har yanzu Gwamnan Adamawa bai kammala aiki ko daya ba, a cewar jam’iyyar APC.
Jam’iyyar na kuma zargin Gwama Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP da kasa kaddamar da ko da aiki daya a jihar.
Skataren APC reshen jihar Adamawa Wafanri Theman ya ce saboda haka shekara daya na gwamnatin PDP bata lokaci ne a jihar.
APC ta kuma ce mulkin PDP suna ne jihar saboda tafiyar hawainiyarta wurin gudanar da ayyuka sabanin gwamnatin APC.
“Dukkanmu mun ga abin da APC ta yi a baya amma PDP ta ba da kunya.
“Mutane sun so su ga bambanci wurin samun cigaba amma gwamnatin nan ba ta himma”, inji shi.
Ya ce APC ta shugabanci jihar a lokacin matsin tattalin arziki amma duk da haka a shekaranta na farko ta yi manyan ayyuka.
Don haka a cewarsa PDP mai ci a yanzu ba ta da hujjar kasa kammala ko aiki daya a shekara guda na mulkinta.
A martaninsa, Gwamna Umaru Fintiri ya ce batun kammalam ayyuka ba matsalar jam’iyyar APC ba ce.
Ya kara da cewa gwamantin PDP a jihar ba ta sayar da kwangiloli yadda ya zargi APC da yi a baya.
Gwamnan ya ce ayyukan da gwamantinsa ke yi manya ne masu wa’adi mai tsawo kammlawa.
Gwamnan ya ce ayyukan cigaba ba su takaita ga gine-gine ba kawai, sun shafi kyautata rayuwar jama’a.
A cewarsa iyalai sun shaida ayyukan cigaban gwamnatinsa ta hanyar samun tallafin naira 15,000 zuwa 30,000.
“Ba aikinsu ba ne bayan sun kasa su je suna surutai a kan matsalar da ba ta shafe su ba, inji gwamnan.