A ranar Lahadin da ta gabata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika shekara guda tun bayan da ya sha rantsuwar kama aiki, a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015, bayan ya lashe zaben watan Maris din shekarar 2015. Kuma jam’iyyarsa ta APC ita ce take da galibin ’yan majalisa da ke Majalisar kasa da gwamnoni 23 da kuma galibin ’yan majalisar dokokin jihohi.
Kamar yadda Buhari ya bayyana da kansa, ’yan Najeriya sun sanya manyan buri a kan sabuwar gwamnatinsa. Jam’iyyar PDP da ta mulki kasar nan na tsawon shekara 16 ta barnatar da dimbin arzikin kasar nan. Ba ta yi shugabanci nagari ba, ta yi almubazaranci, da rashin hukunta masu laifi da kuma aikata magudin zabe. Jam’iyyar ta sha kayi ne a zaben da ya gabata saboda Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a wato (Card Reader Machine), wadda ta sanya da wuya a iya magudin zabe.
Shin ko Shugaba Buhari ya iya biyan manyan bukatun ’yan Najeriya? Eh da kuma a’a amsoshi ne biyu da ake iya samu. Idan muka fara da bangaren masu cewa Eh, Shugabancin Buhari ya samu nasara kan babbar matsalar da take ci wa kasar nan tuwo a kwarya a bara, wato rikicin Boko Haram. Kodayake, gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta yi kokari wajen kwato manyan garuruwan da suke hannun ’yan Boko Haram, amma kaimin kungiyar bai ragu ba, ko bayan da Shugaba Buhari ya kama mulki. Gwiwowin sojoji sun yi sanyi kuma ba su da isassun kayan aiki, cin hanci ya yi kaka-gida a shugabancin dakarun, inda ake samun bore.
Yadda Buhari ya sauya abubuwa a kasa da shekara guda wani abu mai kama da al’ajabi. An samu galaba a kan Boko Haram. Ba ta da manyan makaman da kuma shugabanci. Ta koma wata karamar kungiya da ta gudu daga wannan kauye zuwa wancan. Sojojin kasa da na sama suna aikin tare da ’yan kato da gora inda suka shiga dajin Sambisa kuma ma har sun ceto ’yan mata biyu daga cikin ’yan matan makarantar Chibok da aka sace.
Sunan da Buhari yake da shi na yaki da cin hanci da ayyukan rashawa ya kara gyara sunan Najeriya a cikin kasar nan da tsakankanin kasashen duniya da kuma bayanan ayyukan cin hancin da gwamnatin da ta gabace ta yi. Ba a taba ganin yadda aka karkatar da kudin al’ummar kasar nan ba zuwa aljihunan wasu tsiraru, kamar yadda ya faru zamanin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan. Batun cewa Buhari ya bankado masu cin hanci ya kara farfado da kimar kasar nan a idon ’yan Najeriya a karon farko cikin lokaci mai tsawo. kasashen duniya kansu sun yin maraba da Buhari, inda suke cewa shi ne shugaban kasar nan da ya bambanta da na baya.
Farin jinin da Shugaba Buhari yake da shi ya sa gwamnatinsa ta dauki wadansu manufofi gwamnati marasa farin jinni, misali shi ne kara farashin man fetur. A baya babu wani abu da ’yan Najeriya suka tsana kamar karin kudin mai, amma lokacin da gwamnatin Buhari ta dauki wannan mataki galibin ’yan Najeriya sun ki fita tituna don shiga zanga-zanga duk da yunkurin da kungiyar kwadago (NLC) ta yin a ganin hakan ya faru.
Shugaban ya tarar da farashin gangar danyen mai ya fadi kasa warwas, wanda hakan ya jawo raguwar kudin shiga ga matakan gwamnatoci guda uku da ake da su. Galibin jihohi ba sa iya biyan albashin ma’aikatansu. Hakan ya sa gwamnatin tarayya ta ba su bashin kudi don warware matsalar ta hanyar Babban Bankin kasa (CBN). Saboda karancin kudin kasashen ketare, darajar Naira ta fadi a kasuwannin bayan fage, yayin da CBN yake kokarin biyan bukatun masu shigo da kayayyaki kasar nan. Wadannan matsaloli sun sa kasar nan tana gab da fada wa matsalar tattalin arziki.
Gwamnatin Buhari ta samu nasara ta fannin tsaro da farfado da kimar kasar nan da yaki da cin hanci, amma akwai jan aiki a fanin tattalin arziki. Maganar gaskiya shi ne wannan matsalar za ta iya mayar da hannun agogo baya ga sauran nasarorin da aka samu.
Kwanakin baya ne cibiyar kasuwanci a Jihar Legas ta yi korafi kan cewa gwamnatin Buhari ba ta wani tsari kan tattalin arziki. Kuma wannan shi ne galibin ra’ayin jama’a masu bibiyan al’amura. Gwamatin ba ta da manyan manufofi da tsare-tsaren tattalin arziki da kuma masana ta fuskar tattalin arziki. Jinkirin zartar da kasafin kudin bana ya sa matsalolin sun kara tabarbarewa. Fanin tattalin arziki yana matukar bukatar a mayar da hankali a kansa sosai, saboda kada ta mayar da sauran ci gaban da aka samu baya.
A yanzu haka, farashin gangar mai ta tashi zuwa Dala 50 saboda ayyukan tada kayar baya da suka dawo a yankin Neja-Delta, kasar nan ba ta iya fitar yawan gangar man da ta saba fitarwa. Wata kungiyar ce da take kiranta Niger Delta Abengers take fasa bututan mai, wanda kuma hakan ya jawo karancin wutar lantarki a kasar nan. Zuwa yanzu Shugaba Buhari ya tunkari matsalar da matakan soji amma muna masu ba shi shawara da ya hada da matakan siyasa wajen warware ta.
Nan zuwa badi, manyan kalubalen da ke gaban Buhari su ne magance matsalar tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan da wadata kasar nan da wutar lantarki da kammala yaki da Boko Haram da tabbatar da cewa miliyoyin ’yan gudun hijira sun koma muhallinsu da magance matsalar kungiyar Niger Delta Abengers da magance matsalar satar mutane don neman kudin fansa da ta satar shanu da kuma tabbatar da tsayuwar yaki da cin hanci. Muna taya shugaban kasa murnar cika shekara guda a kan mulki, muna mai fatan ci gaba da samun nasara.
Shekara guda bayan hawan Buhari
A ranar Lahadin da ta gabata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika shekara guda tun bayan da ya sha rantsuwar kama aiki, a ranar…