✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara daya da rasuwar M.D.Yusufu: Ban kwana da kundin tarihi mai rai

Makabartar   dan takum  da ke  birnin  Katsina ta  samo  asali ne  daga  wani malami  masani addini musulunci kuma  Waliyyi,  mai  suna Muhammad  ibn  Ahmad  At …

Makabartar   dan takum  da ke  birnin  Katsina ta  samo  asali ne  daga  wani malami  masani addini musulunci kuma  Waliyyi,  mai  suna Muhammad  ibn  Ahmad  At  Tazakhat.A  nan ne  aka  rufe  M.D. Yusufu.
A gefen  kabarinsa daga  hannun  dama kabarin  mahaifiyarsa ne Hajiya  Hadiza,wadda  ta rasu  shekaru goma da suka wuce.Daga  hagu kuma  kabarin  yayarsa  ce  Hajiya  Akila.
Shi  ya  zabi  wajen da aka rufe  shekaru  sha biyar  da suka  wuce.Kuma an  ce wani  lokaci ya kan kai ziyara wajen,yana  kuma sawa  a je  ziyara wurin,  wanda  ya  kira  da sunan gidansa  na karshe  a duniya.
Daga  bakin  kabarin ta  gabas   za ka  iya hango  dakinsa  da ke  gidansa  na Katsina,amma  wani  dogon bene  da aka yi  ya  kare shi. Daga  nan  zuwa  gidansa  tafiya ce  ‘yan mintuna a kasa.
Gidansa.yana  unguwar  da ake  kira  Yaranci, wadda Sarki  Dikko ya  kafa ta. Titin da gidansa  yake, sunan  kakansa ne aka sanya  masa, watau Muhammad  Dikko  Road.  Lamba na  49. Daga nan ana  iya  hangen gidan  Mahaifinsa.  Magajin gari Yusufu.
Gidan  M.D Yusufu  na  Katsina an gina  shi  da konannen bulo (Red bricks). Duk Katsina   shi ne aka fara  ginawa  da  irin  wannan bulo.Ginin  bene  ne  hawa  daya. A kasan benen, bangare  daya  dakin karatu ne.wanda  littafan  da ke  ciki  sun fi  na  babbar  laburaren  jahar Katsina. Wani dakin  kuma jaridu  ne iri-iri na tsawon shekaru,wadanda aka hada  su  littafi-littafi, su ma sun cika  dakin.Sai  dan  wajen  da yake  ganawa  da  mutane,wanda bai iya daukar mutum  goma  lokaci  guda.
A  gidansa  na  Legas,littafai da jaridu  da  muhimman  takardu ne  suka  canye  kashi  biyu cikin  uku  na gidansa. Tirela-tirela  aka  rika  cikawa ana kai wa  Cibiyar  Yusufu Bala Usman da ke  Zariya, a lokacin  da  zai  baro  Legas  da zama.
A  gidansa na  Abuja ma  tun daga   falonsa, Litattafai da jaridu ne kewaye   da shi.daya daga cikin ‘ya‘yansa rasa  daki ya yi, sai  dai ya  rika  rabawa a dakin karatu yana  kwana.
Duk  wani littafi  da  ya zo masa sai  ya  karanta shi. Idan kuma  ya ji labarinsa zai sa a nemo masa ya  karanta.Babu  wani  littafi  da  aka rubuta  wanda ya shafi Najeriya  ko Afirka  da  bai da shi, sai dai  idan marubucin in  wani dan dagaji ne. Idan littafi  ya  fito ya karanta za ka ji  yana sharhin cewa, abin da marubucin  ya fada  haka ne  ko kuwa  da kuskure.Wani lokaci ya kan buga wa  marubucin waya ya ce  na ga  littafi  kaza, amma abu kaza da kaza a cikin littafin ba haka ba ne.
Duk  wadansu  muhimman abubuwan da suka faru a tarihin Najeriya a gabansa aka yi, yana  da cikakkiyar masaniyar yadda aka yi. Idan kana magana  da shi zai ba ka misalai na shekaru  hamsin, ya  rika  gangarowa har zamanin da  kuke,sai  ya yi  sharhi ya kuma fitar da mafita.
Manyan  shaihunan ilmi tarihi a kasar  nan sun sallama  cewa shi  wani  tushe  ne wanda za ka san  gaskiyar me ya faru a  tarihin siyasa da mulkin  Najeriya. Shaihunan malamai irinsu. Farfesa  Abdullahi Mahdi, shugaban jami’ar  jahar  Gombe da Farfesa Alkasum Abba, shugaban jami’ar  jahar  Adamawa da  Dakta Abubakar Saddik na jami ar ABU Zariya da Dakta  Patric  Wilmot, kadan ne daga cikin shaihunnan malaman da  suka  sallama  masa.
Ba ya  tarayya da kowa sai  wanda  ya san ciwon kansa ko ya san abin da yake yi ko mai wani kyakykyawan guri da alkibla. Duk wasu masana da manazarta a kasar nan sun san da zamansa. Idan  kuma  ya  dauke ka domin ku yi tafiya tare,ba ya nuna bambanci,ya kan ce ka koyi mu’amala da  manya  don wata rana ba sa nan, kai ke nan.
Na  taba samun kaina muna  mitin a waje guda  lokaci  guda a shekarar 2002, ga  marigayi  Dakta  Yusufu  Bala Usman ga marigayi Farfesa Sam Aluko ga Malam  Sani Zoro ga dakta Abubakar  Saddik. Na kalliteburin, na kalli kaina, na kalli wanda ya tara mu marigayi M.D.Yusufu. Da jikina ya yi  tsami  sai na dauko biro da  takarda na rubuta dan  wake,  kamar  haka:
In an tambaye ki  ina ina?
Fada masu ina  a cikin  giwaye
Fada  masu  ina tsakiyar  zakoki,
Fada  masu  ina gaban  dakaru
Fada masu na zama  jinjiri ana mani  tatata.
Fada masu ina a wani zama na tarihi.
A gabana marigayi  Uche Chukumeiriji a lokacin yana  Sanata, ya zo aka tsara yadda za a wargaza  shirin da wasu ke yi na kawo tazarcen  Obasanjo a  Majalisar  dattawa. Idan aka tattauna sai a dawo wajen M.D.Yusufu, wani  lokaci ya soke duk  tsarin da aka yi ya sake sabo,wani  lokaci kuma ya canza masa fasali. Sai na sake wani rubutun  kamar  haka:
Tarihi  yana  aukuwa ne  da  mutane.
Tarihi yana  faruwa ne da bigire,
Tarihi  yana aukuwa ne da lokaci.
Tarihi yana da ‘yan  taka rawa da kuma ‘yan kallo.
A  inda  nike tarihi ne zai faru.
A  wurin  ina  kallo,ina taka rawa da bayar da rowan sha da kuma gurzo takarda. Ina  daukar darasin da babu wani aji da za a iya samunsa.
M.D. Yusufu mutum ne mai karfafa gwaiwar adana tarihi da bincike,wannan ya sanya ya sha daukar nauyin assasa wajen adana kayan tarihi da bayanan tarihi. Ya yi tsaye wajen ganin an gina Cibiyar Yusufu Bala Usman da ke Hanwa  Zariya.
Idan  ya  ba ka  littafi  zai  tambaye ka me ka fahimta. Idan ka kawo masa littafi zai tabbatar ya karanta, idan akwai abin gyara a ciki ya gyara.  
Ya  taba ba ni aron littafi,bayan wani lokaci ya bukaci abinsa. Ina Katsina ya  sanya na hau jirgi na kai masa a Legas. Ya ce hau jirgi ka koma gida. Na ce masa yallabai littafin fa Naira uku aka saye shi,sai ya ce idan za ka samo mun shi a kasuwa zan saya Naira dubu 500.Ya ce, ai babu inda za ka sameshi ko nawa ne. Ya ce, kana lissafin kudin jirgi ne da tasin da ka hau,ni  kuma ina lissafin idan ya sallwanta ina zan samo  shi? domin wanda ya rubuta shi ya  mutu, kamfani kuma babu shi. Ko a lokaci kwafi dari  biyar kacal aka buga.
A shekarar 2013 da na ce masa za mu kafa cibiya  mai suna: M.D.Yusufu  Research  and  Documentation Centre.sai  ya kura  mani idanu, sannan ya ce idan kun ga ya dace  to Allah Ya ba da sa’a, taku ce. Don ni tawa  ita ce  Yusufu  Bala Usman Centre  da ke Zariya.
Ganina na karshe da shi, shi ne lokacin da na je gidan ya ce in dauki wata mujjala mai suna The  Atlantic, ya ce,  ‘je ka karanta da safe mu tattauna  a kan labarin da suka kawo.’
M.D.Yusufu ya tafi ya bar tarihi jibge a cikin dimbin littafai da kuma tarin takardun da ya bari.Amma tarihin da ya tafi da shi a kwakwalwarsa yana da yawan gaske. Allah Ya jikansa.

danjuma Katsina Marubuci kuma danjarida. 08035904408. email mdanjumakatsina@gmail .com