✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara daya bayan haduwa, matashi ya yi wa ‘kawar Facebook’ fyade

Ta ce sun fara haduwa da matashin ne a shafin sada zumunta na Facebook

’Yan sanda a Jihar Ogun sun cafke wani matashi mai suna Ebenezer Adeshina saboda yi wa wata yarinya fyade da kuma yin barazanar sakin hotunanta na tsiraici.

Matashin, mai kimanin shekara 25 ya shiga hannu ne bayan budurwar, mai shekara 16 ta kai shi kara ofishin ’yan sanda na Owode Egbado da ke Jihar.

Ta ce sun fara haduwa da matashin ne a shafin sada zumunta na Facebook a shekarar 2021.

Ta shaida wa ’yan sanda cewa sun fara hira da shi ne da farko, kafin daga bisani wayarta ta lalace, inda ya kirata yana yi mata alkawarin biyan kudin gyaran wayar.

A cewarta, Ebenezer ya bukaci ta zo gidan shi ta karbi N3,000 don gyaran wayar.

Ta ce bayan zuwan nata gidan ne ya ba ta abin sha mai dauke da kwaya har ta fita hayyacinta, inda ya dauki hotunanta ma tsiraici.

Rahoton da ’yan sanda suka fitar ya ce, “Bayan ya yi lalata da ita lokacin da ta fita daga hayyacinta, sai wanda ake zargin ya dauki hotunanta, yana barazanar sakin su a kafafen sada zumunta idan ba ta biya shi N50,000 ba.”

Kakakin ’yan sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labarai cewa an kama shi ne bayan sun bi sahun wanda ake zargin.