✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 9 da sace Daliban Chibok, har yanzu 98 na hannun Boko Haram

Kawo yanzu 178 daga cikin Daliban Chibok da Boko Haram ta sace a 2014 sun kubuta, babu labarin inda sauran 98 suke

Yau ’Yan Matan Chibok suke cika shekara tara a hannun kungiyar Boko Haram da ta yi garkuwa da su.

A daren ranar 14 ga watan Afrilu, 2014 mayakan Boko Haram suka kutsa Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Chibok a Jihar Borno suka sace dalibai 276 da ke shirin rubuta jarabawar kammala sakandare.

Sace daliban shi ne irinsa na farko a Najeriya, wanda ya fi girgiza Najeriya tare da janyo wa gwamnati matsin lamba daga cikin gida da kasashen waje domin ganin ta ceto su.

In banda 25 daga cikin daliban da suka tsere a lokacin da mayakan ke tafiya da su, ba a sake jin duriyar daliban da aka sace ba sai bayan shekara biyu, lokacin da ’yan banga suka gano Amina Ali, daya daga cikin daliban a kusa da Dajin Sambisa.

Daga baya Maryam Maiyanga da danta tare da mijinta wanda dan Boko Hatay ne suka tsere; Sai wasu biyu da kowacce ta tsere.

Daga bisani gwamnati ta samu ceto karin 21 daga cikin daliban ta hannun kungiyar Red Cross wadda ta shiga tsakanin kungiyar da gwamnatin.

Sai a 2017 Boko Haram ta sako karin dalilai 82.

Zuwa yanzu dai 178 daga cikinsu sun kubuta daga hannun kungiyar, inda suka dawo a kanjame, suna bayyana irin bakar wahalar da aka gana musu, wasunsu kuma dauke da ’ya’ya da suka haifa wa mayakan kungiyar.

Sai dai kuma har zuwa yanzu 98 daga cikin daliban suna hannun kungiyar, babu cikakken labarin halin da suke ciki.

’Yan Matan Chibok sun shiga jami’a

Ana iya tunawa baya sako daliban, Gwamnatin Tarayya ta dauki nauyinsu inda sanya su a Jami’ar Amurka da ke Yola, wasu kuma ta kungiyoyin kasashen waje suka dauki nauyinsu.

Daga cikinsu, Lydia Pogu, ta kammala karatun digiri na biyu a a Jami’ar  Southeastern da ke kasar Amurka a watan Mayun 2022.

Ta samu wannan ne shekara guda bayan ta kammala digirinnta na farko a fannin Shari’a da Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar.

A wani jawabi da ta yi a madadin sauran Daliban Chibok a lokacin bikin kammala digirin farko, Lydia ta ce ba ta taba zaton za ta iya komawa makaranta ba, saboda irin barazanar da ’yan Boko Haram suka yi mata.

Suna bukatar taimako —Nkeki

Shugaban kungiyar iyayen daliban, Yakubu Nkenki, ya ce daga cikin yara 107 da aka dauki nauyi a karkashin shirin, 84 sun samu zuwa jami’a amma wasu 23 sun daina zuwa makaranta a yayin da wasu daga cikinsu da suka yi aure suka dakatar da karatun domin kula da jariran da suka haifa.

Da yake kira ga gwamnati ta yi duk abin da ya kamata domin a ceto ragowar yaran da ke hannun Boko Haram, Yakubu Nkenki, ya kuma bukaci gwamnatin da ta tallafa wa wadanda suka daina zuwa jami’ar don su samu abin dogaro da kansu da kuma kula da ’ya’yansu.

Ya yaba bisa kokarin da gwamnati ta yi a kan ’ya’yan nasu, yana mai cewa suna da kyakkyawa game da alkawrin Shugaba Buhari na ganin sun samu rayuwa mai inganci.

Amma ya bukaci a tallafa wa wadanda suka fice daga makaranta saboda, “mata ne ’yan shekara 25 zuwa 27, idan aka bar su a kauye rayuwarsu na iya shiga cikin hadari.”

Ya bayyana damuwarsa cewa karin mutum 14 daga cikin daliban da aka gano a yayin da dubban mayakan Boko Haram da iyalansu suka mika wuya ga sojoji, an bar su a Maiduguri maimakon zuwa da su Abuja a ba su kulawa kamar yadda aka yi wa wadanda aka ceto a baya.

Akwai tsangwama

Nkeki ya bayyana cewa wasu daga cikin daliban suna fuskantar tsangwama a cikin al’umma, inda sau uku ana kai wa ’yan sanda kara a garin Chibok, saboda ana kiran su ’yan Boko Haram.

Daya daga cikin daliban da ta nemi kada a ambaci sunanta ta ce an sha zagin ta, amma ba ta taba kai wa hukuma kara ba.

“Mutane sun sha kira na matar Boko Haram, wani lokaci kuma nakan ji su suna gulma ta; abin da zafi, amma ban taba tankawa ba,” in ji ta.

Sakatren kungiyar iyayen daliban, Lawal Zanna, ya ce har yanzu suna sa ran yin tozali da roguwar ’ya’yan nasu.

Don haka ya roki gwamnati da kada ta yi kasa a gwiwa har sai duk yaran sun dawo.

Amma ya bayyana damuwa cewa mulkin Shugaba Buhari na dan da karewa, ga shi kuma har yanzu ’ya’yan nasu na hannun Boko Haram.