A yau ne fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Muhamamd Auwal Adam Albany, ya cika shekara takwas da rasuwa bayan ’yan bindiga sun yi masa kisan gilla.
Sheikh Auwal Albany ya koma ga Mahalliccinsa ne a sakamakon wani hari da wadansu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka kai masa, inda suka bude masa wuta tare da iyalansa.
A ranar Asabar 1 ga watan Fabrairu, 2014 ne aka samu labarin mahara sun bi motar babban malamin, a lokacin yana tare da matarsa da kuma dansa suka bude musu wuta suka kashe su nan take.
An yi wa Sheikh Auwal Albany kisan gilla ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gidansa da ke Gaskiya Layout a unguwar Tudun Jukun da ke Zariya.
Hakan ta faru ne bayan ya kammala karatun da yake gabatarwa na littalin Sahihul Buhari a makarantar Markaz da ke uguwar Tudun Wada Zariya.
Rasuwar Sheikh Albani ta dade tana girgiza al’ummar Musulmin Zariya da na sassan duniya.
Rasuwar fitaccen malamin ta kasance ne shekara 11 bayan kisan gilla da aka yi wa abokinsa kuma babban malamin Musulunci, Sheikh Ja’far Mahmud Adam, wanda aka bude wa wuta a yayin da yake limacin Sallar Asuba a masallacin gidansa da ke unugwar Dorayi a Kano.
A lokacin rayuwarsa, Sheikh Adam Albany ya taka muhimmiyar rawa wajen amfani da karatuttukansa domin wayar da kan Musulmi, musamman matasa, game da muhimmancin rungumar neman ilimin addini da na boko da kuma kaiwa matuka a cikinsu, gami da kyawawan dabi’u domin ci gaban al’umma.
Ya kasance mutum ne mara tsoro wajen tsage gaskiya a kowane lokaci, kuma ya yi abin a yaba ta hanyar mayar da hankali wajen koyar da yadda ake gudanar da ayyukan ibada a aikace da kuma yin gyara ga wasu kura-kuran da ake aikatawa.
Marigayi Sheikh Albany, ya zama abin koyi a sassan Najeriya a bangaren gabatar karatuttuka ta hanyar nuna cikakkiyar siffar yadda ake gudanar a ayyukan ibaba ta bidiyo. Ya kuma yi cikakken tsarin daukar sautin karatun da yake gabatarwa domin samun cikakkiyar fa’ida ga duk wanda ya saurara.
Karatun da ya gabatar na ‘Sifatu Salatun Nabiy…’ (Siffar Sallar Manzon Allah (SAW) da ‘Alhkamul Jana’iz’ (Hukunce-Hukuncen Jana’iza) da sauransu a aikace sun taimaka kwarai da gaske, inda har aka rika sanyawa a masallatai domin jama’a kulla su kuma koya.
Kafin rasuwar Sheikh Albani a wa’azozin da yake gabatarwa, yana yawan yin magana a kan hadin kan Musulmai, kuma mutuwar tasa ta nuna an amsa wannan kira da yake yi, domin kuwa a wajen jana’izarsa babu maganar bangare na addini.