A ranar Juma’a aka gurfanar da wasu mata guda biyu a gaban wata Kotun Majistare dake Ikorodu a jihar Legas bisa zargin hada baki su daki wata amarya a gidan mijinta.
Wadanda ake zargin, Ruka Tayo da Jimoh Abiola dai na fuskantar tuhuma ne bisa zargin hada baki wajen aikata laifi da kuma cin zarafin amaryar, duk da yake sun musanta hakan.
- Yadda muka dakile yunkurin sace dalibai a makarantar ’yan Turkiyya a Kaduna – sojoji
- Dalibai 39 ne ba a gani ba bayan harin Kaduna
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa daya daga cikin wadanda ake zargin tsohuwar matar mijin amaryar da suka lakadawa dukan ce.
Dan Sanda mai shigar da kara a gaban kotun, ASP Gbemileke Agoi ya shaidawa kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne ranar 26 ga watan Fabrairun 2021 da misalin karfe 4:00 na yamma a gidan amaryar dake rukunin gidaje na Mowowole a Ikorodun.
Ya ce matar ta hada kai da abokiyar tuhumarta ne wajen aikata laifin a kan amaryar tsohon mijin nata shekaru biyar bayan rabuwarta da shi.
Dan sandan ya ce laifukan sun saba da tanade-tanaden sassa na 412 da 172 na Kundin Manyan Laifuka na jihar Legas na shekarar 2015.
Alkalin kotun, Mai Shari’a R.A Onilogbo ya amince ya bayar da belin wadanda ake tuhumar a kan kudi N50,000 tare da mutane biyu da za su tsaya musu.
Daga nan sai ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 31 ga watan Maris na 2021.