✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 43 a sarauta: ’yan dambe sun fafata don taya Sarkin Zazzau murna

A ranar Lahadin da ta gabata ce ’yan  wasan damben gargajiya suka fafata dambe don taya Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris murnar cika…

A ranar Lahadin da ta gabata ce ’yan  wasan damben gargajiya suka fafata dambe don taya Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris murnar cika shekara 43  a gadon sarauta.  

Damben gargajiyar da ake yi a kowane yammaci a gidan wasan kwallon kafa da ke Club Street a Sabon Gari, ya cika makil da hakimai da dagatai da masu unguwani da ’yan kallo, inda fitattun ’yan wasa dambe daga sassan kasar nan suka hallara.

’Yan wasa daga Arewa da Kudu da Jamusawa da Gurumada wadanda suka fito daga jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da Kano da Jigawa sun fafata a wasanni daban daban. 

A kawarar Autan Fafa da Garkuwan Shagon Alabo, Autan Fafa ya kashe Shago Alabo a zagaye na biyu, sannan danladi Na-Geza Gurumada ya kashe Gyelon Auta Sakido a zagayen Farko, yayin da ba a samu kisa ba a fafatawar Shagon Shamsu da danlami Na-Dogon Auta.

Sarkin makadan dambe dan Moyi daga Sakkwato da Garkuwa Ma’azu dan Anace daga Zamfara sun kawata filin wasan da kidin dambe.  

Bayan kammala wasa a tsakanin gogaggun ’yan wasa Aminiya ta ji ta bakin mai masaukin baki, kuma mai gidan dambe, Anas Sadauki dan Sarkin Fawa inda ya ce,sun gayyaci baki manyan ’yan wasan damben gargajiya daga kowace kusurwa na kasar nan ne domin su kai wa Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris gaisuwa da kuma taya shi murnar cika shekara 43 a gadon sarauta. “Domin mu kawata bikin a garin na Zariya, to alhamdulillahi domin bukatarmu ta biya manyan ’yan wasa su yi dambe a gaban wakilan Mai martaba Sarki, kuma sun ji dadi, kuma jama’a da dama su ji dadin kallo. Fatarmu a koyaushe masu sha’awar kallon wasan damben gargajiya su ci gaba da ba mu hadin kai, kuma muna fata a tashi lafiya,” inji shi.

Wanda ya jagoranci hakimai zuwa kallon damben Makaman Zazzau, Alhaji Umaru Mijinyawa cewa ya yi, “Mai martaba ya aiko ni da sakon godiya tare da nuna farin cikinsa domin yadda jama’a suka zo daga sassan kasar nan domin su taya shi murnar cika shekara 43 a gadon sarauta. Kuma Mai martaba ya nemi a ci gaba da yi masa addu’a a koyaushe kuma yana fata Allah Ya mai da kowa gida lafiya.”