✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 10 manyan ayyuka 114 sun gagara kammaluwa

Ana bukatar kashe Naira biliyan 218 a kan ayyukan da ka bayar daga 2009 zuwa 2019 a Jihar Ogun

Kwamitin bitar manyan ayyukan da aka faro daga 2009 zuwa 2019 da Gwamnatin Jihar Ogun ta bayar ya ce jihar na bukatar Naira biliyan 218.4 domin kammala aikin.

Ya gabatar ga rahotonsa ga Gwamna Dapo Abiodun ranar Talata, shekara guda bayan gwamnan ya ba shi aikin.

Kwmatinin nazarin ayyukan kakashin tsohon Shugaban Kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya, Adekunle Mokuolo, ya ce ya bibiyi ayyuka 114 da kudinsu ya kai Naira biliyan 349.4.

Mokuolu ya ce Gwamnatin Jihar Ogun ta riga ta kasha biliyan 130 daga cikin kudaden ayyukan.

Ya ce kashi 88% na ayyukan na ababen more rayuwa ne, daya na noma, biyu na lafiya, uku na ilimi, daya na gidaje sai kuma biyu na ciniki da masana’antu.

Shugaban kwamitin ya ce sun yi cikakken nazari kan bin ka’idojin kwarewa da bin dokoki da tsare-tsare da bayanan aiwatar da ayyukan, kamar yadda yake kunshe cikin rahoton da ya mika wa gwamnan dauke da shawarwarin yadda za a kawo wa jihar cigaba mai dorewa.

– Sai an rika ririta kudin gwamnati –

Gwamna Abiodun ya yaba da aikin kwamitin yana mai cewa zamanin bayar da kwangila yadda gwamnoni suka ga dama ya wuce.

“Yana da kyau mu samu nagartaccen tsarin fitar da dukiya kafin fara duk wani aiki.

“Dole ne yanzu da babu isassun kudade a yi hattar a ririta abin da ke hannu.

“A matsayinmu na gwamnati, muna tabbatar wa jama’a cewa za mu ci gaba da aiwatar da muhimman ayyuka a fadin jihar, musamman wadanda za su amfani jama’a kai tsaye.

Ya ce hakan ce ta sa ya nada kwamitin bitar ayyukan na shekarun 2009 zuwa 2019 domin tsara yadda za a yi nasarar kammala ayyukan da za su yi tasiri wurin samar da shugabanci na gari a jihar.