’Yan wasan kungiyar kwallon kafa ’yan kasa da shekara 17 ta Najeriya, Golden Eaglets, sun bukaci Gwamnatin Jihar Kuros Riba ta cika alkawarin kyautar gidajen da ta yi musu da shugabannin kungiyar bayan sun lashe kofi a 2013.
Tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba, Liyel Imoke ne ya yi wa kungiyar alkawarin a wurin liyafar da ya shirya musu lokacin da suka ziyarce shi domin nuna masa kofin.
- Wasan Najeriya da Saliyo: ’Yan kallo ba za su shiga filin wasa ba
- An yi garkuwa da mashawarcin Gwamnan Sakkwato
“’Yan wasan nan ba a kwana biyu sai sun tunatar da ni alkawarin gidaje da aka yi musu a Kalaba”, inji Babban Mai horas da kungiyar, Manu Garba.
Imoke ya yi alkawarin ba kowane dan wasan Golden Eaglets da masu horas da su gida a Rukunin Gidaje da ke Akpabuyo, amma har yanzu gwamnatin jihar ba ta cika alkarin ba.
Ya ci gaba da cewa “shekara kusan 10 ke nan da yin alkawarin amma har yanzu shiru kake ji”.
Manu Garba ya ce yakan bayyana wa ’yan wasan cewa har yanzu yana kan tuntubar Gwamnan Kuros Riba mai ci, Ben Ayade domin a cika alkawarin da magabacinsa ya yi wa kungiyar.
A nasa bangaren, Mai horas da kungiyar, Musa Muhammed, ya ce a gaban Ministan Wasanni na wancan lokaci Aminu Maigari aka yi alkawarin.
“Tun ina yi wa matasan bayani ina lallashin su cewa su kara hakuri har na kai makura na rasa abin da zan ce musu”, inji shi.