Babban Limamin Masallatan Harami Sheikh Abdul Rahman al-Sudais, ya sanar da dawowar Sheikh Yasser Dossary da wasu limamai biyu.
Sheikh Sudai ya sanar cewa Sheikh Yasir zai ci gaba da limanci a Masallacin Harami da ke Makkah.
Sauran limamn biyu, Sheikh Khalid Muhanna da kuma Sheikh Ahmad Hudhaify, za su ci gaba da limanci ne a Masallacin Manzon Allah Sallal Lahu Alaihi Wa Sallama da ke Madina.
Sheikh Sudai, ya roki Allah “Ya yi musu jagora Ya ba su dacewa a cikin limancinsu ga al’ummar Musulmi,” in ji sanarwar da Hukumar Gudanarwar Masallatai Masu Alfarma ta fitar.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Rashin Wutar Lantarki Ke Durkusar Da Sana’o’i
- An tsare mutane 300 a gidajen yarin Kano ba bisa ka’ida ba —’Yan Sanda
Wannan albishir daga Sheikh Sudais ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin fara azumin watan Ramadan na bana.
A baya dai ana fargabar malaman ba za su yi limanci ba a watan Ramadan, saboda karewar wa’adin kwantiraginsu na shekara huɗu a masallacin.
Da haka adadin limaman masallacin Harami zai sake komawa 8 kamar haka:
1- Sheikh Abdur Rahman As Sudais
2- Sheikh Abdullah Awad Al Juhany
3 – Sheikh Maher Al Muaiqly
4- Sheikh Bandar Baleelah
5- Sheikh Faisal Ghazzawi
6- Sheikh Saleh Al Humaid
7- Sheikh Usaamah Khayyat
8- Sheikh Yasser Dossary
Shekarar 2015 Sheikh Dawsary ya fara limancin sallar Taraweeh a Masallacin Harami a matsayin bakon liman, kafin shekarar 2019 Masarautar Saudiyya ta nada shi a matsayin cikakken limami, wanda za a rika sabunta kwangilarsa bayan shekara hudu.