✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Sani R/Lemu da Umar Sani Fagge sun zama farfesoshi

Fitattun malaman sun zama farfesoshi a Jami'ar Bayero da ke Kano.

Fitattun malaman Musulunci a Kano, Dokta Sani Umar Rijiyar Lemu da Sheikh Umar Sani Fagge sun zama Farfesoshi.

Jami’ar Bayero da ke Kano ta daga matsayin manyan malaman zuwa Mataimakan Farfesa ne saboda gudunmawarsu a bangaren ilimi da bincike da kuma ci gaban Tsangayar Adabi da Ilimin Addinin Musulunci (FAIS).

Wani jami’i a ofishin rajistaran Jami’ar Bayero, inda fitattun malaman suke koyarwa, ya tabbatar da karin matsayin da aka yi musu da ma wasu malamai.

Jami’ar ta kuma yi karin girma ga wasu Mataimakan Farfesa zuwa matsyin Cikakkun Farfessohi a wadannan fannoni kamar haka:

 1. Shehu Ahmad – Harshen Larabci
 2. Aminu Lawal Auta – Harsunan Najeriya
 3. Usman Sani Abbas – Ilimin Addinin Musulunci
 4. Sani Ayagi – Ilimin Addinin Musulunci
 5. Umar Abdulkadir – Ilimin Addinin Musulunci.

Wadanda aka yi wa karin girma zuwa Mataimakan Farfesa kuma su ne:

 1. Umar Sani Rijyar Lemo – Ilimin Addinin Musulunci
 2. Umar Sani Fagge – Harshen Larabci
 3. Aliyu Harun – Ilimin Addinin Musulunci
 4. Nura Sani – Ilimin Addinin Musulunci
 5. Isa Yusuf Chamo – Linguistics
 6. Aishatu Umar – Sashen Ingilishi
 7. Tijjani M. Naniya – Tarihi
 8. Muhammad Wada – Tarihi
 9. Umma Aminu Inuwa – Harsunan Najeriya
 10. Maryam Mansur Yola – Harsunan Najeriya
 11. Halima Abdulkadir Dangambo – Harsunan Najeriya
 12. Ahmad Salisu – Harshen Larabci
 13. Matabuli Shehu Kabara – Harshen Larabci

Akwai kuma wasu karin malaman da su ma Jami’ar ta yi wa karin a  tsangayar zuwa matakai daban-daban bisa la’akari da gudunmuwarsu.